Budurwa Ta Kammala Digiri, Ya Sha Alwashin Rushe Gidansu Na Kasa Sannan Ta Gyara Shi

Budurwa Ta Kammala Digiri, Ya Sha Alwashin Rushe Gidansu Na Kasa Sannan Ta Gyara Shi

  • Wata budurwa mai digiri ta yada hotonta a kofar wani gidansu na kasa, inda ya ci alwashin maida shi katafare na azo-a-gani
  • Wannan hoto dai ya girgiza intanet, domin jama'a da dama sun shiga tambayar shin kammala girgiri ne zai sa ta iya hakan
  • Wasu kuwa alfahari da ita suke, inda suke mata fatan alherin cika burinta da ma murnar kammala karatun nata

Wata matashiyar da ta kammala karatunta na digiri ta ba da mamaki a kafar sada zumunta yayin da dauki hoto a gaban wata bukka da tace gidansu ne.

Sai dai, budurwar bata zo da wasa ba, domin kuwa ta sha alwashin sauya wannan gidan bukka ya zama katafaren gida, lamarin da ya girgiza jama'a.

Mai digiri ta sha alwashin rushewa da sake gina gidansu
Budurwa Ta Kammala Digiri, Ya Sha Alwashin Rushe Gidansu Na Kasa Sannan Ta Gyara Shi | Hoto: Squad Magazine
Asali: Facebook

Mujallar Squad ce ta yada wannan hoton a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

Cikin karfin gwiwa, budurwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mama, na kammala... Yanzu zan iya daukar nauyin gina gida mai kyau ga ahalina."

Martanin 'yan soshiyal midiya

Wannan batu na mai digiri ya jawo cece-kuce da muhawara a shafin Facebook, ganin yadda aiki ke da wahalar samuwa a nahiyar Afrika.

Kasancewarta 'yar Afrika ta Kudu, 'yan kasar sun yi muhawarar cewa, ba abu ne mai sauki ba daga kammala karatu mutum ya samu aiki.

Ga dai kadan daga martanin jama'a:

Sabuntawar Butho Vuthela ya ce:

"Mun gode da kika iya tuna inda kika fito daga nkosazana, Ki ci gaba da kokari."

Victor Mgidi ya ce:

"Wannan kuskure ne, rigar kammala digiri ba za ta taimake ki wajen iya dauke dukkan bukatun kudi ba."

Kedibone Lenah Malope ya ce:

"Ilimi dai mabudi ne ga nasara komin dadewansa...Ina addu'ar Allah ya cika miki burinki, ina miki fatan alheri."

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

Florence Modisha tace:

"Allah ya miki albarka 'yar uwa. Imaninki da ALlah zai sauya komai. Ki yarda da Allah a kowane yanayi, shi zai bude miki hanyoyin arziki"

Dawn Botha yace:

"Ina son wannan hoton. Allah ne ya dafa miki a tsawon lokaci... Alheri na nan tafe a nan kusa."

Ti Mdz yace:

"Gaskiya kin shajja'ani, kin kyauta bakar yariniya."

Khumo Wa Moshate yace:

"Inda kika fito ba abin dubawa bane, idan lokacinki ne to naki ne. Ina taya ki murna." "

Sylvia Mavela yace:

"Ina maki fatan alheri wajen wannan gini, masoyiya."

Bidiyon Yadda Matashi Ya Kera ‘Wheelbarrow’ Mai Amfani da Inji, Ya Ba da Mamaki

A wani labarin, duniya na kara ci gaba, a yanzu dai 'yan dako sun kusa daina amfani da karfi wajen tura amalanken daukar kaya saboda wani mutum ya samo musu sauki.

Wani bidiyon da @graphicsengineering ya yada a TikTok ya nuna kirkirar wani bawan Allah, inda aka ga yana gwada wata amalanke mai inji.

Kara karanta wannan

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

Lokaci zuwa lokaci, an ce mutumin kan yada bidiyon yadda aikinsa na kirkirar amalanke mai inji ke tafiya daki-daki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel