Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

  • Wani dan Najeriya ya fashe da kuka wiwi bayan ya gano cewa budurwarsa yaudararsa kawai take yi
  • A wani sakon murya da ya yadu a WhatsApp, ya fashe da kuka yayin da yake korafi kan lamarinsa
  • Ba wai yaudararsa kawai tayi ba, harma ta rigada tayi baiko da wannan saurayin da take cin amanarsa da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani dan Najeriya ya fashe da kuka mai tsuma rai bayan ya gano cewa an rigada an yi baikon budurwarsa da wani.

Matashin a cikin wani sakon murya da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, ya ba da labarin mawuyacin halin da ya shiga yayin da yake bayyana cewa baida masaniya game da cin amanarsa da take yi.

Matashi da budurwa
Matashi Ya Fashe Da Kuka Wiwi Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Wani bidiyo ya nuno shi yana kuka wiwi bayan wani ya kwace masa budurwar tasa.

Kara karanta wannan

Sai Kace A Kakkara: Dan Najeriya Ya Koka Da Ganin Masaukinsa A Turai, Ya Wallafa Bidiyon Gidan

A cewarsa, ya zata har yanzu suna tare, bai san cewa ta rigada ta shirya amarcewa da wani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani ya bidiyon

Da suke martani kan lamarin, jama’a sun lallashi matashin da ya mayar da hankali wajen inganta rayuwarsa.

I_amloveday ya ce:

“Fadawa tarkon soyayya da mutumin da bai dace ba na iya kaika inda baka yi tunani ba.”

De_majestic1 ya rubuta:

“An bashi kalaci mai kyau.”

Nellynells__ ya ce:

“Wanda bai taba cin kalaci bane zai yiwa wani ba’a, yi hakuri.”

Misschidel ta ce:

“Abun zai kai kan kowa.”

Ikehnancy_ ta ce:

“Lokacinka na cin kalaci ne yayi. Ka ji tsoron wanda ba a taba kasa shi a soyayya ba.”

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

Kara karanta wannan

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

A wani labarin, jama’a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wani mutum dan yana nuna yadda yake iya tuka tsadaddiyar babbar motarsa duk da kasancewarsa dan tsurut.

Mutumin mai suna Katuosis Babayao ya yada bidiyon don cire kokwanto a zukatan mutanen da ke tunanin ba zai iya tuki ba ko kuma wadanda ke mamakin ya yake tuka motar.

A cikin bidiyon, Babayao ya nuna yadda aka kera masa kujerarsa na zaman tuki zuwa na musamman. Kujerar ta fi ainahin kujerun motoci da aka saba gani tsawo domin bashi damar ganin hanya da kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel