Wata 6 babu Albashi: Ma’aikacin Jami’a Ya Kashe Kan shi Saboda Zafin Rayuwa

Wata 6 babu Albashi: Ma’aikacin Jami’a Ya Kashe Kan shi Saboda Zafin Rayuwa

  • Carter Oshodin yana aiki ne a jami’ar UNIBEN da ke Kudancin Najeriya, a makon jiya ya bar Duniya
  • Jami’an ‘yan sanda sun ce wannan Bawan Allah ya mutu ne a sanaddiyar hallaka kan shi da kan shi
  • Mutanen Umelu a garin Benin suna makokin rasa Oshodin wanda kafin yanzu ma’aikacin jami’a ne

Edo - Wani ma’aikaci a jami’ar tarayya da ke garin Benin watau UNIBEN a jihar Edo, ya kashe kan shi saboda masifa da zafin rayuwa.

Rahoton Premium Times yace daga cikin matsalar da aka samu shi ne wannan Bawan Allah ya gagara biyan kudin makarantar ‘ya ‘yansa.

Wannan mutumi da aka bayyana da Carter Oshodin yana aiki a jami’ar ta UNIBEN, wanda sun shafe watanni ba tare da an biya su albashi ba.

Kara karanta wannan

ASUU: Wasu Daliban Jami’a Sun Hada-kai, Sun Yi Karar Buhari da Ministoci a kotu

Gwamnatin tarayya ta dakatar da albashin ma’aikata da malaman jami’a ne a dalilin yajin-aikin da suka shiga tun a farkon wannan shekarar.

Daga baya sauran ma’aikata sun janye yajin-aikin da suke yi, amma wannan bai sa an biya Carter Oshodin da abokan aikinsu kudinsu ba.

Marigayin yana aiki ne a matsayin malamin shigar da bayanai a wani sashe na jami’ar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

UNIBEN
Jami'ar Benin Hoto: uniben.edu.ng
Asali: UGC

Vanguard take cewa abin takaicin ya faru ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba 2022 a unguwar Umelu a yankin Sokponba a birnin Benin.

Hukumar lafiya ta Duniya watau WHO tace kimanin mutane 703, 000 ake rasa a Duniya a aannan yanayi, kullum ana rasa mutum kusan 2000.

Mutane 1000 sun rasu

Ana asarar mutum Hukumar lafiya ta Duniya tace kimanin mutane 703, 000 aka rasa a Duniya a wannan yanayi, kullum ana rasa mutum 3000.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

Kakakin ‘yan sanda na Edo, Chidi Nwabuzor ya shaidawa manema labarai ma’aikacin ya mutu a sanadiyyar hallaka kan shi da kan shi.

Chidi Nwabuzor yace ‘yanuwan Carter Oshodin sun dauke gawarsa tun a makon da ya gabata.

Ina Tinubu ta samu kudi?

Kun ji labari Dele Alake yace tun can Bola Ahmed Tinubu ba fakiri ba ne, da kudinsa ya shiga takarar 'Dan Majalisar Dattawa a lokacin zaben 1992.

Darektan Kwamitin Kamfe na APC yace Bola Tinubu ya rika sayen hannun jari ne yana saidawa, da haka ne ya zama babban mai kudi Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel