Boko Haram: 'Yan Matan Chibok 98 Suka Rage a Hannun 'Yan Ta'adda, Hukumar Soji

Boko Haram: 'Yan Matan Chibok 98 Suka Rage a Hannun 'Yan Ta'adda, Hukumar Soji

  • Hukumar sojojin Najeriya ta ce har yanzu akwai sauran yan matan Chibok 98 tsare a hannun yan ta'addan Boko Haram
  • Zuwa yanzu rundunar ta bayyana cewa yan mata 178 ne suka kubuta cikin 276 da yan ta'addan suka yi garkuwa da su a 2014
  • Rundunar Operation Hadinkai ta kuma ce daga watan Yuni zuwa yau, an kama mutum 113 da ke kaiwa yan ta’addan abinci, taki da sauran kayan amfani

Borno - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa har yanzu akwai sauran yan matan makarantar Chibok guda 98 tsare a hannun yan ta’addan Boko Haram.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne yan ta'addan suka farmaki makarantar firamare ta yan mata da ke Chibok a jihar Borno inda suka sace dalibai 276.

Shugaban sashin bayanan sirri na rundunar Operation Hadinkai da ke yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas, Kanal Obinna Ezuipke, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Maimalari a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu

Sojoji
Boko Haram: 'Yan Matan Chibok 98 Suka Rage a Hannun 'Yan Ta'adda, Hukumar Soji Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Ezuipke wanda ya bayyana adadin yan matan da aka ceto ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Daga cikin yan matan Chibok 276 da aka sace, yan mata 57 sun tsere a 2014 yayin da aka saki yan mata 107 a 2018. An ceto yan mata uku a 2019, biyu a 2021 sannan an ceto 9 a 2022, wanda jimilarsu ya zama 178 sun kubuta yayin da 98 suka yi saura a hannun Boko Haram.”

Da yake bayar da jawabi kan ayyukan dakarun Operation Hadinkai a Agustan 2022, Kanal Ezuipke ya bayyana cewa an kashe jimilar yan ta’adda 43, yayin da sojojin suka kama wasu 24 a watan Agusta kadai, baya ga sama da 100 da aka kashe a watan Satumban 2022.

Har ila yau, ya ce an kwato makamai da suka hada da bindigogin AK-47 129, alburusai 1,515, bindigogi 16 da sauransu.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo

Ezuipke ya bayyana cewa sojojin sun samu hare-hare 26 daga yan ta’addan, kuma a cikin haka, an kashe sojoji biyu kuma wasu 9 sun jikkata.

Ya kara da cewa sojojin sun aiwatar da fatrol 2726 da kautan bauna 982 kan yan ta’addan.

Da yake martani kan kamun masu kaiwa Boko Haram kaya, Ezuipke ya bayyana cewa daga watan Yuni 2022 zuwa yanzu, an kama mutum 113 da ke kaiwa yan ta’addan abinci, taki da sauran kayan amfani.

Ya bayyana cewa dakarun sun kuma ceto mata da yara da dama, sun kuma lalata kayayyaki da mabuyar yan ta’addan, rahoton Daily Post.

Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo

A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wani Isiyaku Babangida, kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Kananan Yara 3 Sun Mutu A Ginin Da Ya Rufta A Jigawar Tsada

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jaridar The Cable ta rahoto.

A cewar Shehu, an kama Babangida ne a yayin wani aiki da jami’an tsaro suka gudanar a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel