Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu

Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu

  • Dakarun tsaro a Kaduna sun yi nasarar kashe wasu yan bindiga cikin gungun wadanda suka kai hari a NDA tare da sace sarkin Bungudu da wasu hare-haren
  • Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kaduna ya sanar da hakan inda ya ce sojoji sun yi artabu da yan bindigan ne a karamar hukumar Chikun
  • Aruwan ya ce wadanda sojojin suka kashe sun hada da Musti, mataimakin Boderi, Yellow Mai-Madrid da Dan Katsinawa da wasu da ba a riga an gano sunansu ba

Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce dakarun sojojin Najeriya sun kashe yan bindigan da suka kai hari makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna, The Cable ta rahoto.

An rahoto cewa jami'an sojoji biyu sun rasa ransu yayin harin da yan bindigan suka kai a makarantar a watan Agustan 2021.

Taswirar Jihar Kaduna.
Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaron cikin gida, ya ce sojojin sun yi artabu da yan bindigan ne a kusa da tollgate a karamar hukumar Chikun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya - Aruwan

Kwamishinan ya ce Boderi Isiya, 'hatsabibin' dan bindiga wanda aka ce shine shugaban gungun yan bindigan ya sha kyar.

Sanarwar da ya fitar ranar Asabar ta ce:

"Bincike da sahihan bayanan sirri sun sake tabbatar da cewa Boderi da yan tawagarsa na ta'addanci sun ci ba dadi a hannun dakarun tsaro.
"A cewar rahoton, sojojin sun yi musayar wuta da yan bindigan kusa da Tollgate a karamar hukumar Chikun. Yan bindigan sun tsere, suka sake fada wa hannun wasu dakarun a Sabon Gida.
"Sojojin suka bude musu wuta, kuma suka ci galaba kansu.
"An gano gawarwaki da makamai daga wurin, yayin da wasu yan ta'addan suka mutu sakamakon harbin bindiga."

Ya kara da cewa:

"Mataimakin Boderi, wani Musti, yana cikin wadanda aka halaka, tare da wani Yellow Mai-Madrid da wani Dan Katsinawa, tare da wasu da ba a riga an gano sunansu ba. Wasu yan ta'addan suna nan rai a hannun Allah.
"Musti da Boderi ne suka kai hari a Makarantar Sojoji ta NDA, Kaduna, da sace dalibai daga kwalejin nazarin nazarin gandun daji, da sarkin Bungudu da wasu mutanen da bara."

Kwamishinan ya ce duk wani da ke da bayanai masu amfani game da yan bindigan da za a iya gani suna neman magani ya kira lambobi kamar haka: 09034000060, 08170189999.

DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

A wani rahoton, kun ji yan sandan farin kaya na DSS na cigaba da bibiyan wadanda ke da alaka da Tukur Mamu, wanda ya taimaka wurin sulhu da yan bindiga, a yayin da suka kama surukinsa, Abdullahi Mashi, a daren ranar Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa jami'an yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja, wanda shima an kama shi an kuma dawo da shi Najeriya tare da mawallafin na Desert Herald a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel