'Yan Bindiga Sun Kara Hallaka Jami'an Yan Sanda Kudancin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Kara Hallaka Jami'an Yan Sanda Kudancin Najeriya

  • Miyagun yan bindiga sun farmaki Motar Sintirin yan sanda, sun kashe dakaru uku a jihar Enugu dake kudu maso gabas
  • Bayanai sun nuna cewa ba zato ba tsammani maharan suka bude wa yan sandan wuta a yankin karamar hukumar Enugu ta arewa
  • Hukumar yan sandan jihar tace tuni ta kaddamar da farautar maharan, kuma ta baza komarta ko ina da nufin cafke su

Enugu - Jami'an yan sanda uku sun rasa rayuwarsu yayin da wasu Miyagun 'yan bindinga suka farmake su a New Haven, yankin ƙaramar hukumar Enugu ta arewa a jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 10:15 na dare a wata Tashar Motoci dake yankin.

Kara karanta wannan

Wasu 'Yan Mata 5 Sun Taru Sun Lakaɗawa Kawarsu Dukan Kawo Wuƙa Har Ta Mutu Kan 'Saurayi'

Dakarun hukumar yan sanda.
'Yan Bindiga Sun Kara Hallaka Jami'an Yan Sanda Kudancin Najeriya Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

An ce 'yan bindiga sun buɗe wa dakarun 'yan sandan wuta, suma suka yi kokarin maida martani aka yi musayar wuta. Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin ɗar-ɗar.

Wani ganau, mai Shagon ɗaukar Hoto kusa da wurin da lamarin ya faru, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, yace ga dukkan alamau maharan sun shirya kai wa jami'an hari ne tun farko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yan sanda uku ne suka mutu amma gawar mutum biyu muka gani, sun ce an garzaya da ɗaya Asibiti," inji Mutumin.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da kashe jami'ai uku ga jaridar ranar Alhamis da safe.

Yace Jami'an yan sanda na cikin tafiya a Motar Sintiri, ba zato 'yan bindigan a cikin Lexus SUV, suka farmake su. A cewarsa jami'ai uku sun ji munanan raunuka a musayar wuta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan sanda a wata jiha suka yi zanga-zanga kan wasu dalilai

"Daga baya aka tabbatar da dakarun uku sun rasa rayuwarsu a Asibiti, " Inji Kakakin hukumar yan sandan.

ASP Ndikwe, yace tuni dakarun yan sanda suka baza komarsu ta ko ina da nufin damƙe maharan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Jihar Enugu na ɗaya daga cikin jihohin yankin arewa maso gabas waɗanda a baya-bayan nan lamarin ta'addancin 'yan bindiga ke ƙara taɓarɓarewa.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina

Gwarazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel