'Yan Sanda Sun Yi Zanga-Zanga a Osun Kan Rashin Biyansu Albashin Watanni 18

'Yan Sanda Sun Yi Zanga-Zanga a Osun Kan Rashin Biyansu Albashin Watanni 18

  • Wasu jami'an 'yan sanda a Najeriya sun fito zanga-zanga don nuna bacin ransu ga rashin biyansu albashin watanni 18
  • Kwamishinan 'yan sanda ya fusata, ya ce 'yan sandan sun saba dokar aiki tunda suka fito zanga-zanga haka siddan
  • Hukumomi da kungiyoyi da dama a Najeriya sun sha yin zanga-zanga don neman hakkokinsu a hannun gwamnati

Jihar Osun - Wani rahoto mai ban mamaki ya ce, jami’ai kwanstabul na rundunar ‘yan sanda, a ranar Laraba 7 ga watan Satumba sun yi wata zanga-zanga a jihar Osun saboda rasa albashin watanni sama da 18.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ce, ‘yan sandan sun zagaya a wasu yankunana Osogbo, babban birnin jihar Osun, dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen nuna koke da rashin samun albashi da alawus-alawus, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Da aka zanta da wani dan sanda mai suna Tijani Adewale, ya ce watanni 18 basu sami albashi ba, tun bayan kammala basu horo da aka yi

Yadda 'yan sanda suka yi zanga-zanga a Osun
'Yan Sanda Sun Yi Zanga-Zanga a Osun Kan Rashin Biyansu Albashin Watanni 18 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Adewale ya ce duk da ba a biyansu albashi, sun ci gaba da zama ma'aikatan kirkir ta hanyar nuna jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, yanzu haka jami’an ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a bakin aikinsu, inda ya ce jami’an sun sha yin kokarin yadda albashin zai fito amma abu ci tura.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adewale Olokode ya yi martani game da koken jami'an, ya kuma bukaci jami’an da su tsaya da zanga-zangar tukuna tare da mika kokensu ga hukumomin da suka dace, The Nation ta ruwaito.

A cewar kwamishinan:

“Kuna bata sunan rundunar ta hanyar zanga-zangar da kuke. Kamata ya yi ku kai koken ku ga hukumomin da suka dace.”

Kara karanta wannan

Yan Achaba Na Kwanciya Da Matanmu, Jami’an Yan Sanda Sun Yi Zanga-zanga

“Kawai dai kuna tada zaune tsaye ne ta hanyar yin zanga-zanga. Matukar kuna sanye da wannan kaki, to muna tsammanin ku kasance masu kyakkyawar tarbiyya.”

Bamu samu hakkinmu na kula da zaben gwamnan Osun ba, inji wani jami'i

A bangare guda, wani jami'in da ya nemi a sakaya sunansa ya koka da cewa, ba a biya jami'ai kudaden alawus na kula da zaben gwamnan da aka yi Osun ba a watan Yulin da ya gabata.

A cewarsa:

“Mun yi mu gano dalilin hana mu kudinmu amma mun rasa takamammen bayani mai ma'ana daga hedikwatar rundunar ba.
"Ya saba doka a ce mun yi zanga-zanga don neman alawus-alawus, amma muna rokon sufeto-janar na 'yan sanda da ya duba lamarinmu."

Ma'aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Sun Tafi Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

A wani labarin, gamayyar ma'aikatan hukumar kula da yan sanda PSC ta sanar da tafiya yajin aiki ga shugabanta bisa saba alkawuran da akayiwa ma'aikatan.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

Gamayyar ta bayyana cewa zasu fara yajin aikin ne ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, 2022. Shugaban gammayar, Mr Adoyi Adoyi, ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, rahoton Punch.

Ya ce sun yanke shawarar tafiya yajin ne sakamakon rashin jituwa dake gudana tsakanin shugaba hukumar, Musuliu Smith da Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba, lamarin daukan sabbin yan sanda, karin girma, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel