Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

  • Wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta roki kotu da ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali Garba saboda tsabar jarabarsa
  • Zainab ta tabbatar da cewa mijinta na zuwa gida da tsakar rana a watan Ramadan ya nemi kwanciya da ita, har a lokutan al'adarta
  • Ta sanar da rashin yarda da yake nuna mata kuma baya bata abinci saboda fushin bata kwantawa da shi a azumi ko tana al'ada

Kaduna - Wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta bukaci kotun shari'a dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali garba Ali saboda tsabar jarabarsa.

Daily Trust ta rahoto, mai karar a ranar laraba ta sanar da kotu cewa Garba na neman jima'i ko a lokutan da take al'adan da lokacin azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ya Magantu Kan Kamen Hadiminsa, Tukur Mamu, a Kasar Misra

Rabuwar Aure
Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Zainab tace sun yi zaman aure na shekara daya kacal inda ta kara da cewa ta bar gidansa ne saboda wannan lamarin.

Wacce ke karar ta yi bayanin cewa a yayin zamansu, Garba ya saba dawowa gida har da rana a lokutan da take jinin al'ada don ya kwanta da ita, wanda addinin Islama bai aminta da hakan ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A yayin azumin watan Ramadan, ya saba dawowa gida da rana kuma ya bukaci kwanciya da ni, idan na ki amincewa sai yayi fushi.
"Sannan idan na bukaci abinci, sai yayi martani da cewa in je wurin saurayina ya ciyar da ni.
“Bai taba yarda da ni ba ta yadda baya barin duk 'yan uwana mata da maza su ziyarce ni."

- Ta sanar da kotun

Matar tace ta bar gidan aurenta saboda bata iya gamsar da mijinta saboda tsabar bukatarsa.

Kara karanta wannan

Ban San Ka Ba: Budurwa Yar Najeriya Ta Hana Mahaifinta Halartan Daurin Aurenta, Ta Bayyana Dalili

A don haka ta roko kotun da ta tsinke aurensu saboda bata shirya bin bukatar mijinta ba wurin sabawa Ubangiji.

Mijinta, ya musanta ikirarin inda yace Zainab ta shigar da wadannan zargin a kan sa a kotu daban-daban.

Garba ya sanar da kotun ta bakin lauyansa M.A Sambo cewa, mahaifiyar matarsa ta je har gida sannan ta kwashe kayansa tare da siyarwa daga bisani ta tafi da diyarta.

Yace mahaifiyarta tayi alkawarin dawo masa da komai da ta dauka a gidan a yayin da suka yi wani zaman sasanci.

Garba ya bukaci kotun da ta duba bukatarsa na dawo masa da kayansa kafin ya amince da sakin auren.

Alkali Murtala Nasir bayan sauraron dukkan bangarorin, ya umarci wacce ke karar da ta zo kotu a zama na gaba da mahaifiyarta.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin cigaba da shari'ar.

Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

A wani labari na daban, wata kotu mai matsayi na farko dake yankin Kubwa ta babban birnin tarayya ta kashe aure mai shekaru 19 tsakanin 'dan kasuwa Lukman Abduaziz da matarsa Rashidat kan banbance-bancen da aka gaza shawo kansu.

Alkalin mai suna Muhammad Adamu, ya tsinke auren saboda Abdulaziz ya roki tabbatar da sakinsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Adamu wanda yace a Musulunci mutum yana da damar sakin matarsa yace Rashidat ta sanar da kotu cewa ta kammala iddarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel