Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu

Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu

  • Magidanci ya bayyana sakin matarsa da yayi saboda tsabar tsanar mahaifiyarsa da tayi kuma bata sallolinta 5 na rana
  • Kamar yadda Lukman Abdulaziz ya sanar, ya kauracewa matarsa Rashida kuma a yanzu ta kammala iddarta
  • Rashidat ta sanar da cewa ba za ta bar gidan shi ba saboda tare suka gina a matsayin mallakin yara hudun da suka haifa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Wata kotu mai matsayi na farko dake yankin Kubwa ta babban birnin tarayya ta kashe aure mai shekaru 19 tsakanin 'dan kasuwa Lukman Abduaziz da matarsa Rashidat kan banbance-bancen da aka gaza shawo kansu.

Alkalin mai suna Muhammad Adamu, ya tsinke auren saboda Abdulaziz ya roki tabbatar da sakinsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Adamu wanda yace a Musulunci mutum yana da damar sakin matarsa yace Rashidat ta sanar da kotu cewa ta kammala iddarta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

Kotu da Aure
Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Yace Rashidat ba matarsa bace kuma an shawarcesa da su je su samu lokaci tare da tattaunawa kan yadda zasu tarbiyyantar da yaransu hudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin yace kotu zata bada shaidar rabuwar auren.

Tun farko, Abdulaziz ya sanar da kotun cewa ya kasa shawo kan matsalar dake tsakaninsa da matsar kuma ya sakte amma yana neman tabbaci daga kotu.

“Ba ta yi sallolinta na kowacce rana kuma bata kaunar 'yan uwana. Na bukaci ta bi ni kauye yadda zamu sasanta kan dalilin da yasa bata kaunar mahaifiyata amma ta ki.
"Na saketa a ranar 6 ga watan Yuni kuma ta kammala iddah. A yanzu bani da ra'ayin rayuwar aure da ita kuma na sanar da iyayenta," yace.

A martanin Rashidat, ta sanar da kotun cewa Abdulaziz ya sanar da ita a ranar 27 ga watan Augusta, baya kwanciyar aure da ita na watanni uku da suka wuce saboda yana son sakinta.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

"Yace zai kula da yaranmu hudu amma yana son in bar masa gidansa saboda zai siyar da shi.
"Na sanar masa cewa gidan mallakin yarana saboda tare muka gina, ba gidansa bane," yace.

Saboda Abinci, Matashi Dan Shekara 23 Ya Kashe Kakansa Mai Shekaru 60 Da Wuka

A wani labari na daban, an tsare wani mutum mai shekara 23, Vincent Awonugba a gidan gyaran hali na Olokuta kan zarginsa da kashe kakansa mai shekaru 68, Florence Olaoye, saboda abinci.

Vanguard ta rahoto cewa an gurfanar da wanda ake zargin a kotu kan tuhumar laifi guda daya na kisan gilla, a kotun majistare da ke zamanta a Akure, jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel