Ban San Ka Ba: Budurwa Yar Najeriya Ta Hana Mahaifinta Halartan Daurin Aurenta, Ta Bayyana Dalili

Ban San Ka Ba: Budurwa Yar Najeriya Ta Hana Mahaifinta Halartan Daurin Aurenta, Ta Bayyana Dalili

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Mabel ta hana mahaifinta halartan daurin aurenta da duk wani abu da ya shafeta
  • Mabel ta ce sam ita bata da uba kuma cewa koda wasa kada mutumin mai suna Mista Ilesanmi ya nuna yana da wata alaka da ita
  • A wani sako da ta wallafa cike da dacin rai, Mabel ta ce mahaifinta ya yi watsi da ita tsawon shekaru 27 kuma babu yadda zai dawo rayuwarta a yanzu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Mabel Oluwaninse Wealth, wata budurwa yar Najeriya ta yi fice a shafukan soshiyal midiya bayan ta bukaci mahaifinta da kada ya halarci daurin aurenta.

A cewar Mabel, dalilinta na yanke wannan hukunci na hana mahaifinta halartan wannan babbar rana a rayuwarta shine cewa mutumin ya watsar da ita tsawon shekaru 27.

Kara karanta wannan

'Sharrin Boka Ne' Wata Budurwa Ta Halaka Mahaifiyar Saurayinta Ana Shirin Ɗaura Aure

Mace da namiji
Ban San Ka Ba: Budurwa Yar Najeriya Ta Hana Mahaifinta Halartan Daurin Aurenta, Ta Bayyana Dalili Hoto: Mabel Oluwaninseweath and PM Images/Getty
Asali: UGC

Mahaifin Mabel na rokon kudi a wajenta

A cikin wani sakon tes da mahaifin nata ya aike mata, ya nemi da ta taimaka masa da kudi N5000 don ya siya magani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take amsa sakon, Mabel ta fada masa cikin yanayi na rashin tabbass cewa bata da mahaifi.

Ta tunzura matuka cewa mutumin na so ya dawo cikin rayuwarta bayan ya samu labarin cewa tana shirin yin aure.

Wallafar da tayi a soshiyal midiya na dauke da sakon tes da suka yi musaya da mahaifinta.

Kalli wallafar a kasa:

Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

A wani labari na daban, jama’a sun shiga rudani bayan bayyanar wasu hotuna na manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja da Momee Gombe a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

A cikin hotunan wadanda tuni suka yadu a shafukan sadarwa, an gano jaruman biyu cikin shiga da ta fi kama da ta sabbin ma'aurata kuma sun yi tsayuwar daukar hoto sak irin na amarya da ango.

Wannan al’amari ya jefa mutane cikin shakku, yayin da wasu ke ganin shirin fim ne, wasu kuma sun yi fatan Allah yasa hakan ya zamo gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel