An Kai Makura, Daliban Najeriya Sun Roki Buhari Ya Yi Hakuri Ya Kawo Karshen Yajin ASUU

An Kai Makura, Daliban Najeriya Sun Roki Buhari Ya Yi Hakuri Ya Kawo Karshen Yajin ASUU

  • Kungiyar dalibai ta Najeriya ta nemi shugaba Buhari da ya gaggauta kawo karshen yajin aikin da malamai ke yi
  • Malaman jami'a sun shiga yajin aiki tun watan Fabrairu, hakan ya kawo koma-baya ga fannin ilimin kasar
  • Wata jami'a a Arewacin Najeriya ta yi watsi da batun ASUU, ta ce malamai da dalibai su dawo aikin a makon nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta mika kokenta ga shugaban kasa manjo Muhammadu Buhari mai ritaya da ya yi hakuri ya kawo karshen yajin aikin malaman jami'a ASUU.

Daliban sun roki Buhari da ya daidaita da lakcarorin Najeriya domin ba su damar komawa makaratu su ci gaba da karatu.

Wannan batu na fitowa ne daga bakin shugaban NANS, Kwamared Usman Barambu a Abuja yayin zantawa da manema labarai, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Dalibai sun nemi Buhari ya kawo karshen yajin aiki
An kai makura, daliban Najeriya sun roki Buhari ya yi hakuri ya kawo karshen yajin ASUU | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Barambu ya koka da cewa yajin aikin ya kassara fannoni daban-daban na ilimin jami'o'in gwamnati tare da kawo kari ga shekarun kammala karatu ga dalibai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ka yi amfani da kwarewa ka kawo karshe matsaoli

Shugaban fannin yarjejejiya na NANS, Usman Ayuba ya roki Buhari ya yi amfani da kwarewarsa da ikonsa wajen kawo karshen yajin.

Haka nan, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.

Ya kuma yi kira ga warware matsaloli da dama da suka addabi Najeriya, NewsPress ta tattaro.

Idan baku manta ba, jami'o'in gwamnati a Najeriya sun kasance a garkame tun ranar 14 ga watan Fabrairu, lamari da ya kawo tsaiko ga ilimi a Najeriya.

Dalibai sun sha kokawa, kungiyar ASUU ta ki daga kafa kan bukatun da ta ba gwamnati saboda muhimmancinsu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki

A wani labarin, hukumar gudanarwar jami'ar jihar Gombe (GSU) ta kira dukkan malaman ta bukaci dukkam ma'aikatanta dake hutun karatu da su gaggauta dawowa aiki.

Wannan na zuwa kira na zuwa ne a yau Litinin 5 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Magatakardar jami’ar, Dakta Abubakar Aliyu Bafeto, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Satumba 5, 2022, ya umurci malaman jami'ar da ke karatu a Najeriya da su koma bakin aiki kasancewar jami'ar ta dawo karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.