Mutane 9 Sun Mutu, 10 Sun Jikkata A Mumman Hadarin Mota A Abuja

Mutane 9 Sun Mutu, 10 Sun Jikkata A Mumman Hadarin Mota A Abuja

  • Wani mummunan hadarin mota da ya ritsa da mutane 22 ya faru a hanyar Yangoji zuwa Abaji a birnin tarayya Abuja
  • Hatsarin da ya faru tsakanin wata motar bas kirar Toyota da babban mota ya yi sanadin rasuwar mutum 9, wasu 10 sun jikkata
  • Bisi Kazeem, kakakin yan sanda na Abuja ya ce an kai gawawarikin wadanda suka rasu babban asibitin Kwali kuma an fara bincike

Abuja - Hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, ta bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutum tara yayin da wasu 10 suka jikkata a wani hatsarin mota kan hanyar Yangoji-Abaji, a Abuja, The Punch ta rahoto.

A cewar sanarwar da jami'in wayar da kan mutane na hukumar, Bisi Kazeem ya fitar, hatsarin ya ritsa ne da wata motar bas kirar Toyota Hiace mai lamba KTG-450 KQ a Babban mota kirar Howo Sino misalin karfe 6.05 na safiyar Asabar.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Hukumar FRSC.
Mutane 9 Sun Mutu, 10 Sun Jikkata A Mumman Hadarin Mota A Abuja. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bas din tana zuwa ne daga Jihar Osun a hanyarta na zuwa Jihar Katsina amma ta kutsa wa babban motar da ke tsaye.

Ya ce dukkan motoccin biyu da hadarin ya ritsa da su na haya ne.

Kazeem ya ce:

"Mutum 22 hadarin ya ritsa da su. Dukkansu maza ne. Goma sun jikkata, tara sun mutu. An bada agajin farko ga biyu cikinsu. FRSC ta gano N3,170, jakuna shida da wayoyin salula daban-daban guda hudu.
"Gawar mutanen tara na babban asibitin Kwali kuma yan sanda sun fara bincike."

Jami'in FRSC ya yi martani

A cewar Kazeem, jami'in FRSC, Dauda Biu, ya ce mummunan overtaking ne ya yi sanadin hatsarin, Channels TV ta rahoto.

Biu ya kuma ce an fi mutuwa a hatsarin dare bisa na rana.

Kara karanta wannan

Labari da Duminsa: Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje, Ya Ritsa da Mutane a Legas

Ya ce rundunar za ta cigaba da wayar da kan mutane har sai sakamakon da ake bukata ya samu.

Ya bukaci masu ababen hawa su tabbatar komai lafiyarsa kalau a motoccinsu kafin su hau titi don gudun hatsari musamman da dare.

Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota

A wani rahoton, Kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.

Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel