Labari da Duminsa: Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje, Ya Ritsa da Mutane a Legas

Labari da Duminsa: Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje, Ya Ritsa da Mutane a Legas

  • Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da rushewar wani bene mai hawa bakwai da ake tsaka da ginawa a jihar
  • Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, ginin yana titin Oba Idowu Oniru dake jihar Legas kuma mutum bakwai ya ritsa a ciki
  • Ya tabbatar da cewa, manyan kayayyakin aikin haka na hukumar a halin yanzu ake amfani da su wurin ganin an ceto wadanda lamarin ya ritsa da

Bene mai hawa bakwai da ake tsaka da gininsa a titin Oba Idowu Oniru dake jihar Legas ya rushe inda ya ritsa da mutum shida.

Daily Trust ta rahoto cewa, babban sakataren hukumar again gaggawa ta jihar, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a sa'o'in farko na ranar Lahadi.

Labari da dumi
Labari da Duminsa: Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje, Ya Ritsa da Mutane a Legas
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Tura Shaharren Mawaki Ice Prince Zamani Gidan Yarin Ikoyi

Ya bayyana cewa, an fara kokarin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su.

Yace:

"Bayan isa wurin da abun ya faru, wani bene mai hawa bakwai da ake ginawa ya rushe. Babu wanda ya samu rauni amma mutum shida ake gano ya murkushe kuma ginin ya hana su fitowa.
"Za a bukaci manyan kayan aikin haka na hukumar domin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su. Muna fada aikin gaggawar kuma ana kan yi yanzu haka."

Rushewar Ginin Kano: Tinubu ya Aike wa Ganduje Wasikar Jaje

A wani labari na daban, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan rayukansu da aka rasa a rushewar gini mai hawa uku na kasuwar Beirut a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wasikar da Tinubu ya rubuta zuwa Gwamna Ganduje mai kwanan wata 31 ga Augustan 2022, ya bayyana matukar damuwarsa da tausayawa kan mummunan al'amarin da ya faru.

Kara karanta wannan

Rushewar Ginin Kano: Tinubu ya Aike wa Ganduje Wasikar Jaje

Ya kara da yi wa wadanda suka samu rauni fatan samun lafiya.

"Rushewar bene mai hawa uku da ake ginawa abu ne mai taba rai. Wadanda suka suka rasa rayukansu bai dace su rasu a wannan halin ba.
"A yayin fatan Allah ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu, ina jajanta wa iyalansu da 'yan uwansu. Ina kira garesu da su dauka hakuri tare da rungumar lamarin matsayin kaddara daga Allah," takardar tace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel