Mu Kake Kira Yara, Zamu Koya Maka Hankali: Wike Ya Yiwa Ayu Raddi

Mu Kake Kira Yara, Zamu Koya Maka Hankali: Wike Ya Yiwa Ayu Raddi

  • Rikicin da ya raba kan 'yayan jam'iyyar adawa ta PDP ya dau sabon salo a wannan mako
  • Rigimar ta dawo 'danya yayinda Wike da Shugaban uwar jam'iyya suka fara yiwa juna raddi
  • Gwamna Nyesom Wike ya yi kira ga yan Najeriya kada su yarda da yan takaran jamiyyar PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ikwerre, Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a ranar Alhamis, ya mayar da raddi ga shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Iyorchia Ayu.

Wike yace ai tuni sun gano Ayu kudi N14bn da jam'iyyar ta samu lokacin zaben fidda gwani yako son wawushewa.

Ya siffanta shugaban jam'iyyar ta PDP a matsayin mara godiya kuma mai girman kai saboda ya kirashi karamin yaro.

Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da tituna a karamar hukumar Ikwerre dake jihar ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, 2022.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

Wikey
Mu Kake Kira Yara, Zamu Koya Maka Hankali: Wike Ya Yiwa Ayu Raddi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Yaran da kake kiranmu, mu muka tado ka lokacin da ta kare ma. Ku dubi jam'iyyar dake son cin zabe, zamu taya ku."
"Ayu, kace kai ka kafa jam'iyyar nan, amma ka bar jam'iyyar a 2007. Ka kafa kamfani, sai ka bar kamfanin, wasu sukayi tsayin daka wajen rike kamfanin yau, ba kada hakkin cewa kai ka kafa ta."
"Yan Najeriya sun gani yanzu yadda kuka zama butulu, idan muka baiwa wadannan mulki, shin kuna ganin zasu godewa Najeriya?"

Hakazalika, mamban kwamitin amintattun PDP, Bode George, ya ce jawabin da Iyorchia Ayu yayi bai dace ba.

Yace:

"Ta wani dalili shugaban jam'iyyarmu zai rika kiran zababbun gwamnoni yara. Shin yana tunanin yara basu girma ne? Ya kamata a rike sara ana duba bakin gatari."

"Wasu Tsaffin Janar-Janar Sun Min Barazana Da CIA," In Ji Wike

Kara karanta wannan

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya ce wasu janar-janar din soji masu murabus a kasar suna barazanar za su yi amfani da wadanda suka sani a CIA su ladabtar da shi idan bai yi abin da suke so ba.

Central Intelligence Agency (CIA) wata cibiyyar tattara bayanin sirri na Amurka da aka daura wa nauyin tattara bayanai da nazari a kansu da nufin tsaron kasashe a duniya galibi ta hanyar tattara bayanai ta karkashin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel