"Wasu Tsaffin Janar-Janar Sun Min Barazana Da CIA," In Ji Wike

"Wasu Tsaffin Janar-Janar Sun Min Barazana Da CIA," In Ji Wike

  • Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya yi wata magana mai karfi game da alakarsa da wasu tsaffin Janar din soji a kasar
  • Wike ya ce wasu shugabanni a kasar da suka yi murabus suna masa barazana da cibiyar bincike ta Amurka idan bai yi abin da suke so ba
  • Jigon na PDP ya bukaci janar-janar din su yi amfani da sanayarsu da CIA su magance matsalar Boko Haram a maimakon yi masa barazana da abokansa

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya ce wasu janar-janar din soji masu murabus a kasar suna barazanar za su yi amfani da wadanda suka sani a CIA su ladabtar da shi idan bai yi abin da suke so ba.

Central Intelligence Agency (CIA) wata cibiyyar tattara bayanin sirri na Amurka da aka daura wa nauyin tattara bayanai da nazari a kansu da nufin tsaron kasashe a duniya galibi ta hanyar tattara bayanai ta karkashin kasa.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Nyesom Wike
"Wasu Tsaffin Janar-Janar Sun Min Barazana Da CIA," In Ji Wike. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana a Port Harcourt a ranar Laraba, 31 ga watan Agusta, Wike ya ce abin kunya ne yadda janar-janar din suka gaza amfani da kafa da suke da shi a CIA wurin magance matsalar Boko Haram, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da wasu tituna a Igwurita, Jihar Rivers.

Kalamansa:

"Wasu mutane sunyi barazanar cewa su tsaffin janar-janar ne, wai sun san wasu a CIA na Amurka kuma za su iya ladabtar da mu. Na ce musu, babu matsala.
"Idan kuna da kusanci da CIA ta Amurka, me zai hana ku yi amfani da su ku warware matsalar Boko Haram.
"A jiki na ne za ku yi amfani da shi? Najeriya tana fama da babban matsala kuma kana da kusanci da CIA, kun san su a matsayin tsaffin janar-janar, me zai sa ba za su yi amfani da kusancin su warware matsalar Najeriya ba?".

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana

A bangare guda, an bayyana abubuwan da aka tattauna tsakanin gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinbu, rahoton This Day.

Wike, gwamnan jihar Rivers ya fusata da sakamakon zaben fidda gwani na jam'iyyarsa da kuma rashin zabinsa a matsayin abokin takara da Atiku Abubakar ya ki yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel