Lamari Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Shugaban PDP

Lamari Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Shugaban PDP

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya maida zazafan martani ga shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu
  • Gwamnan ya gargaɗi Ayu da cewa butulci da girman kai ba zai kai shi ko ina ba, idan shi mutun ne ya cika alƙawarin da ya ɗauka
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban PDO Na ƙasa ya ayyana masu kiran ya sauka daga mukaminsa da yara

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, bisa nuna, "Butulci," da "Girman kai" bayan an masa alfarma ya ɗare kujerar shugaban jam'iyya.

Channels tv ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan furucin ne a wurin ƙaddamar da hanyoyin Omereli, yankin ƙaramar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, ranar Alhamis.

Gwamna Nyesome Wike na jihar Ribas.
Lamari Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Shugaban PDP Hoto: @channelstv.com
Asali: Twitter

Daily Trust taa rahoto Gwamna Wike yace:

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, Bola Tinubu Ya Faɗi Yawan Shekarunsa Na Gaskiya, Yace An Shiga Ruɗani

"Zaka iya kwatanta abinda karfin mulki zai yi, abinda butulci zai yi, ta ya mutane zasu zama masu butulci a rayuwarsu, na yi tunanin a matsayin shugaba jam'iyya dake son lashe zaɓe, aikinka shi ne ka kawo zaman lafiya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Karka raba kawunan jam'iyya, kar ka nuna girman kai a jam'iyya. Eh yaran su ne suka ɗora ka a matakin da kake, yaran nan ne suka kai ka matsayin Ciyaman."

Gwamnan ya ƙalubalanci Ayu ya nuna shi mutum ne Dattijo kuma mai gaskiya ta hanyar cika alƙawarin da ya ɗauka na sauka daga kujerar da yake kai idan har ɗan takarar shugaban kasa a PDP ya fito daga arewa.

Ya ƙara da cewa Biliyan N14bn da jam'iyya ta tara lokacin siyar da Fom na zaɓukan fidda 'yan takara a watan Mayu, wajibi a yi adalci wajen amfani da su.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game Da Atiku, Kwankwaso a 2023

Yadda aka matsa wa Ayu lamba

Kalaman Gwamnan sune na baya-bayan nan a kiraye-kirayen da ake ga Ayu kan ya sauka daga kujerar shugaban PDP bayan Atiku Abubakar (Daga jihar Adamawa) ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a watan Mayu.

Mista Ayu, wanda ya fito daga jihar Benuwai a arewacin Najeriya, a watan Okotoba, 2021 yace zai yi murabus daga kujerarsa idan sharaɗin ya cika amma a ranar Laraba ya canza zance, yace ba zai sauka da muƙaminsa ba.

Tun farko, shugaban kwamitin amintattu BoT na jam'iyyar PDP, Walid Jibrin, ɗan arewa daga jihar Nasarawa, ya amince da cewa rashin adalci ne ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su fito daga yanki ɗaya.

A wani labarin kuma Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Kasa Dake Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike

Ana zargin tsoffin gwamnoni biyu daga jihohin Ondo da Kuros Riba da jagorantar rura wutar rikicin Atiku Abubakar da gwamna Wike.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Zai Haɗa Karfi da Atiku, Gaskiya Ta Fito

Bayan su kuma ana zargin wasu tsofaffin Ministoci, wani Sanata da masu ruwa da tsaki a PDP da ƙara wutar rikicin Fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel