Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

  • Peter Obi ya bayyana cewa addu'arsa kullum shine Allah ya taimaka wasa wajen mulki na gari idan yayi nasara a 2023
  • Peter Obi ya ce Allah ya tsine masa da 'yayansa albarka idan ya taba satar kudin gwamnati
  • Peter Gregory Obi ne dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party (LP)

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Amurka - Dan takarar kujerar shugaban kasar na Labour Party ya yi watsi da zargin cewa ya taba satar kudin gwamnati lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.

Yayin jawabi a Beverly Hills dake birnin California, kasar Amurka ranar Talata, 30 ga Agusta, tsohon gwamnan na Anambra yace gaskiya tayi wahala shi yasa mutane basu yarda idan aka fasa musu magana yanzu.

Peter Obi
Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi
Asali: Twitter

Obi yace Allah ya tsine iyalinsa albarka idan ya taba satar kudin al'umma lokacin da yake ofis.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

Yace addu'arsa guda Ubangiji ya taimakeshi yayi mulkin kwarai idan yayi nasara a zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

His words:

Yace:

"Daya daga cikin matsalolin dake muke fuskanta a Najeriya shine na yi mulki a baya kuma da kamar wuya ka samu mai fadin gaskiya."
"Kullun ina tambayan Ubangiji, kada in zama butulu idan ya bani daman jagorantar al'umma."
"Kuma idan na taba satar kudin al'umma da bai halasta ba, da ni da yarana Allah ya tsine mana albarka."

Zaben Kwankwaso da Obi Zai Kara Wa Tinubu da Atiku Karfi Ne a 2023, Makarfi

A wani labarin kuwa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi, ya ce zaɓen Peter Obi na LP da Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP, ɓata kuri'a ne domin zasu kara kafafa APC da PDP ne kawai.

The Cable ta rahoto Makarfi na cewa kamata ya yi Obi da Kwankwaso su koma jam'iyyar PDP domin taimaka wa jam'iyyar a kokarinta na ganin bayan APC a zaɓen shugaban ƙasan 2023.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Kayar Da Wike Da Sauran Takwarorinsa, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara

Da yake jawabi a shirin Sunrise Daily na Channels tv, ranar Talata, Maƙarfi yace ya kamata matasan Najeriya su kula kar su yi kuskuren yanke hukunci cikin fushi da ɓacin rai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel