Hukumar EFCC Ta Kwmaushe Kakakin Majalisar Dokokin Ogun Olakunle Oluomo

Hukumar EFCC Ta Kwmaushe Kakakin Majalisar Dokokin Ogun Olakunle Oluomo

  • Hukumar EFCC ta kame kakakin majalisar dokokin jihar Ogun yayin da ya gaza amsa gayyatar hukumar
  • An ce an kama shi ne a filin jirgin Legas, kuma an tafi dashi domin fara bincike da yi mas atambayoyi
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana komai game da kama shi ba, amma ana kyautata zaton hukumar za ta magantu

Jihar Legas - Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kwamushe kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, Channels Tv ta ruwaito.

An cafke kakakin ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Alhamis, 1 ga watan Satumba a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake birnin Legas.

Majiyoyi sun shaida cewa, jami’an hukumar ta EFCC sun tafi dashi ne domin titsiye shi tambayoyin da suka shafi laifin karkatar da kudi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Hukumar EFCC ta yi ram da kakakin majalisar jihar Ogun
Hukumar EFCC Ta Kwmaushe Kakakin Majalisar Dokokin Ogun Olakunle Oluomo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu, hukumar dai bata ce komai game da kamun ba, ana sa ran za ta fitar da sanarwar dake bayani kan kama kakakin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gayyace shi ya ki zuwa

A bangare guda, majiyar daga EFCC ta shaida Channels Tv cewa, an sha gayyatar kakakin zuwa ofishin EFCC, amma ya ki amsa gayyatar, rahoton Punch.

An ce yanzu dai an kai Oluomo ofishin EFCC na jihar Legas don ci gaba da yi masa titsiyen tambayoyi.

Al'adar hukumar ce ta gayyaci wadanda take zargi da karkatar da kudaden kasa, kana ta kame wadanda suka ki amsa gayyatar ta duk sadda dama ta samu.

Hakazalika, ta kan fitar da sanarwar yadda ta yi kamu da kuma matakin da za ta dauka a gaba.

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Cire Dan a Mutun Kwankwaso Daga Shugabancin PDP a Kano

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

A wani labarin na daban, a yau Litinin 29 ga watan Agusta ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta aje hukuncin babbar kotun tarayya da ta ba Shehu Sagagi shugabancin jam’iyyar PDP na Kano.

Sagagi dai an ce dan a mutun Kwankwaso ne, kuma tsohon gwamnan ne ya yi ruwa da tsaki wajen ba shi shugaban jam'iyyar a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Bayan komawar Kwankwaso NNPP, ana zargin Sagagi da ci gaba da bin tafarki mai gidan nasa, alamrin da ka iya kawo tsaiko ga makomai siyasar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel