Yan Uwansa Sun Cika Alkawari: Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Dan Najeriya Mazaunin Dubai Ya Ja Hankali

Yan Uwansa Sun Cika Alkawari: Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Dan Najeriya Mazaunin Dubai Ya Ja Hankali

  • Wani dan Najeriya mazaunin Dubai ya nuna bidiyon cikin katafaren gidan da yan uwansa suka gina masa a lokacin da yake waje
  • A cikin bidiyon da ya wallafa a TikTok, mutumin wanda ya cika da farin ciki ya taka rawa yayin da ya nuna godiya ga Allah kan sabon gidan da ya mallaka masa
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun taya matashin murna yayin da suka tabbatar da cewar komai ya ji a gidan

Najeriya - Wani matashi dan Najeriya wanda ya dawo gida kwanan nan daga Dubai ya baje kolin cikin kuryar katafaren gidansa.

Matashin dai yana ta turowa yan uwansa kudi domin su taimaka su gina masa gida yayin da shi kuma yake aiki tukuru a kasar Dubai.

Gidan dan Najeriya
Yan Uwansa Sun Cika Alkawari: Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Dan Najeriya Mazaunin Dubai Hoto: TikTok/Vicsly10
Asali: UGC

Cikin sa’a, yan uwan nasa sun rike amana sannan basu yi almubazaranci da kudinsa ba, don ya dawo ya tarar da wani katafaren gida.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

A cikin wani sabon bidiyo, mutumin wanda ya cika da farin ciki ya taka rawa a cikin katafaren gidan nasa yayin da yake nuna godiyarsa ga Allah da yan uwansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon na dauke da rubutu kamar haka:

“Yan kwanaki bayan Mista Aku ya dawo daga Dubai ya kasance cikin farin ciki. Yana jin dadinsa a cikin sabon katafaren gidansa. Godiya ga Allah da hadadden katafaren gidansa.

Jama’a sun yi martani a kan bidiyon

@slimmamaprecious ta yi martani:

"Kuma sai kaji suna babu kudi a dubai."

@trinacunningham49 ta ce:

"Ina sha'awar kujerun gidan."

@ogochukwueleodimu ya ce:

"Tunda dai kana farin ciki kuma na tayaka gode Allah kan wannan yan uwa da kake da su, ina fatan Allah yasa kada ka nuna abubuwa da yawa game da kanka, miyagu na koina. Allah ya albarkace ka."

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Allah Ya Sauya Labarina: Dan Najeriya Da Ya Taso Cikin Talauci Ya Keta Hazo, Bidiyonsa Ya Yadu

A gefe guda, wani dan Najeriya mai suna Ayo Martins ya isa kasar waje duk da cewar ya fito daga gidan talakawa.

Da isarsa filin jirgin sama na Manchester da ke kasar Birtaniya, sai Ayo ya je shafinsa na TikTok don wallafa bidiyon tafiyarsa, yana bayar da cikakken bayani kan yadda rayuwarsa ta sauya. Ya ba mutane da dama karfin gwiwa.

A cikin bidiyon da ya wallafa, Ayo ya ce ba a haife shi a cikin kudi ba, amma Allah ya sauya labarinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel