Allah Ya Sauya Labarina: Dan Najeriya Da Ya Taso Cikin Talauci Ya Keta Hazo, Bidiyonsa Ya Yadu

Allah Ya Sauya Labarina: Dan Najeriya Da Ya Taso Cikin Talauci Ya Keta Hazo, Bidiyonsa Ya Yadu

  • Wani matashi dan Najeriya mai suna Ayo Martinsa ya bayar da labarin rayuwarsa da yadda Allah ya daukaka shi daga talaka zuwa mai arziki
  • Ayo wanda ya je shafin soshiyal midiya don wallafa wani bidiyo na dan karamin shagon mahaifiyarsa wanda da shi ne aka rainesa kuma yanzu ya samu damar zuwa kasar waje
  • Matashin ya tabbatar da cewar ba a haife shi a gidan kudi ba duk da ya wallafa bidiyonsa yana hanyar zuwa waje, hakan ya taba zukatan mutane da dama

Wani dan Najeriya mai suna Ayo Martins ya isa kasar waje duk da cewar ya fito daga gidan talakawa.

Da isarsa filin jirgin sama na Manchester da ke kasar Birtaniya, sai Ayo ya je shafinsa na TikTok don wallafa bidiyon tafiyarsa, yana bayar da cikakken bayani kan yadda rayuwarsa ta sauya. Ya ba mutane da dama karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

2023: Ba shan romo yasa nake son gaje Buhari ba, Tinubu ya fadi tanadinsa ga 'yan Najeriya

Dan Najeriya
Allah Ya Sauya Labarina: Dan Najeriya Da Ya Taso Cikin Talauci Ya Keta Hazo, Bidiyonsa Ya Yadu Hoto: TikTok/@ayomartinz.
Asali: UGC

Ayo ya jinjinawa mahaifiyarsa a shagonta

A cikin bidiyon da ya wallafa, Ayo ya ce ba a haife shi a cikin kudi ba, amma Allah ya sauya labarinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon mai taba zuciya ya kuma nuno mahaifiyarsa wacce aka gano a cikin dan karamin shagon kwantenanta wanda daga nan ne ta kula da Ayo wanda a yanzu ya samu damar tafiya kasar waje.

Ayo ya ce wata rana, ai bayar da cikakken labarin yayin da ya sumbaci mahaifiyarsa.

Ya rubuta a cikin bidiyon:

“An haifeni a gidan talakawa, amma Allah ya yanke shawarar daurani a saman duk gwagwarmayar da na sha da iyaka. Wata ran azan bayar da cikakken labarin. Barka da zuwa sabuwar rayuwa.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Busking 12 ta ce:

“Kada ka je ka manta da mama a gida faaa! Ka ga yadda ka bar gida.”

Kara karanta wannan

Dan Shekaru 71 Ya Koma Makarantar Firamare, Bidiyo Ya Nuno Sa A Aji Tare Da Jikokinsa

@user7715797646978 ya yi martani:

“Allah ya yi albarka kuma yak are maka ita don ta ji dadin haihuwarta kuma ina addu’a Allah yasa sabuwar kasa da ka shiga ta zamo maka alkhairi.”

Budurwa ‘Yar Najeriya Na Biyan N335k Na Hayar Daki Daya Duk Wata A UK, Ta Yi Bidiyon Cikin Gidan

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ke zama a Birtaniya ta bayyana yawan kudin da take biya na hayar gida mai daki daya a kasar wajen.

Da take bidiyon dan karamin gidan, budurwar ta bayyana cewa a duk wata tana biyan hayar £399 (N335,033.118). Gidan na dauke da dan karamin gado a gefe daya.

Wani bangaren na dauke da tebur da dan karamin allo na karatu. Budurwar ta bayyana cewa a nan ne take wasa kwakwalwarta. Ta bayyana cewa bandakinta na da kyau sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel