Saboda Abinci, Matashi Dan Shekara 23 Ya Kashe Kakansa Mai Shekaru 60 Da Wuka

Saboda Abinci, Matashi Dan Shekara 23 Ya Kashe Kakansa Mai Shekaru 60 Da Wuka

  • An gurfanar da wani matashi, Vincent Awonugba a kotu a Akure kan zarginsa da halaka kakansa mai shekaru 60 a duniya
  • Abdulateef Sulaiman, dan sanda mai gabatar da kara ya fada wa kotu cewa wanda ake zargin ya daba wa kakansa wuka a wuya ne yayin da suke jayayya kan abinci
  • Awonugba, dan shekara 23 ya musanta zargin da ake masa yana mai cewa makwabtansu ne suka alakanta shi da mutuwar kakansa don sun san sun saba rikici

Ondo - An tsare wani mutum mai shekara 23, Vincent Awonugba a gidan gyaran hali na Olokuta kan zarginsa da kashe kakansa mai shekaru 68, Florence Olaoye, saboda abinci.

Vanguard ta rahoto cewa an gurfanar da wanda ake zargin a kotu kan tuhumar laifi guda daya na kisan gilla, a kotun majistare da ke zamanta a Akure, jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matashi ya siyar da mota da wayoyin uban gidansa, ya shiga hannu

Taswirar Ondo
Alkali Ya Ce A Ajiye Masa Matashin Da Ya Kashe Kakansa Saboda Abinci A Gidan Yari. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Yan sanda sun kama Vincent ne kan kashe marigayiyar da wuka a ranar 6 ga watan Agustan 2022, a gidanta da ke Labata Orimolade, jihar Ondo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Vincent, wanda ba a saurari tuhumarsa, shima ya halarci kotun ba tare da lauya mai kare shi ba.

Dan sanda mai shigar da kara, Abdulateef Suleiman, ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ya caka wa marigayiyar wuka a wuya yayin da suke jayayya kan yawan cin abinci da yawonsu da ta ke zargi.

Laifin, a cewar dan sandan mai shigar da kara, Sulaiman, ya saba wa sashi na 316 da 319 na Criminal Code, Cap. 37, Vol. 1 na dokar Jihar Ondo ta Najeriya, 2006.

Sulaiman ya roki kotun ta tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a samu shawara daga ofishin DPP.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin

Yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi ikirarin bai aikata laifin ba, ya kara da cewa makwabtansu ne suka alakanta shi da mutuwar kakansa don sun san sun saba rikici.

Hukuncin Alkali

Alkalin kotun, Tope Aladejana, a hukuncinsa, ya bada umurnin a cigaba da tsare wanda ake zargin a gidan yarin Olokuta kafin a samu shawara daga DPP.

Ya kuma daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Satumba.

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel