Matashi Ya Tattaro Mota da Wayoyin Uban Gidansa Ya Siyar, Zai Tafi Turai

Matashi Ya Tattaro Mota da Wayoyin Uban Gidansa Ya Siyar, Zai Tafi Turai

  • Wani matashi ya tattara mota da wayoyin uban gidansa ya kai kasuwa da nufin tara kudin tafiya Turai
  • 'Yan sanda sun kama matashin tare da wasu mutane uku da ake zargin tare suka hada baki wajen tafka satar
  • Rundunar 'yan sanda na ci gaba bincike domin gano gaskiyar lamari, ya zuwa yanzu dai matashin na tsare

Jihar Legas - Wani matashi dan shekaru 21 mai suna Temple Samuel ya shiga komar rundunar 'yan sandan jihar Legas bisa laifin sata tare da siyar da mota kirar Lexus ES 330 ta ubangidansa a unguwar Ogba dake jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wata wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Legas, Premium Times ta ruwaito.

Ya shaida cewa, jami’an rundunar Rapid Response Squad (RRS) na jihar Legas ne suka kama matashin tare da abokansa uku.

Yadda matashi ya sace mota da wayoyin mai gidansa
Matashi ya tattaro mota da wayoyin uban gidansa ya siyar, zai tafi turai | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar Hundeyin:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An kwamushe Samuel ne a yankin Ogba na jihar tare da wasu mutum uku: Benjamin Bassey dan shekara 32, Chukwuemeka Okorie dan shekara 29 da Joshua Agboche dan shekara 37 da suka hada baki da shi suka siyar da motar."

Hakazalika, sanarwar ta ce matashin ya tsere da motar da cikinta akwa wayoyi kirar iPhone X da iPhone 13 kana ya sace kudi N75,000 daga asusun maigidan nasa, rahoton Vanguard.

Yadda ya siyar da motar

Yayin bincike, matashin ya ce ya siyar da motar ne da nufin tattara kudaden da zai tsallaka dasu kasar waje.

Hundeyin ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Abiodun Alabi, ya ba da umarnin mika batun matashin zuwa sashin binciken manyan laifuka (SCID) dake Panti domin ci gaba da gano gaskiya.

'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dillalin Bindiga Zai Tafi Jihar Zamfara

A wani labarin, rahoton da muke samu ya ce, jami'an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar kama wani da ake zargin kasurgumin dan harkallar bindiga ne a ranar Laraba 31 ga watan Agusta a birnin Gusau.

Jaridar Daily Nigerian ta ce, wanda ake zargin sunansa Sa’idu Lawal mai shekaru 41, ya kuma kasance kofur a rundunar sojojin Najeriya.

An kama shi ne a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna lokacin da yake dauke da bindigu biyu da harsasai da kuma mujallu guda takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel