Matarka Ce? Bidiyon Mai Hoto Da Ya Kamo Wata Amarya Ta Baya Ya Haddasa Cece-kuce

Matarka Ce? Bidiyon Mai Hoto Da Ya Kamo Wata Amarya Ta Baya Ya Haddasa Cece-kuce

  • Wani mai daukar hoto ya ketare iyakar aikinsa bayan wani sabon ango ya caccake shi a yayin daukar hotunan bikinsu
  • A kokarinsa na nunawa angon yadda zai rike amaryar don daukarsu hoto, mai hoton ya cafko amaryar ta baya cike da shauki
  • Sai dai kuma, sam hakan bai yiwa angon dadi ba inda ya gaggauta ture shi daga gefen masoyiyar tasa ba tare da bata lokaci ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani mai daukar hoto ya sha caccaka daga jama’a sakamakon wani abu da ya yiwa wata amarya wanda bai kamata ba a yayin daukar hotunan aurensu.

Wasu sabbin ma’aurata ne suka dauko hayar mai hoton domin ya zo ya dauki hotunan shagalin bikin nasu.

Amarya da ango da mai hoto
Matarka Ce? Bidiyon Mai Hoto Da Ya Kamo Wata Amarya Ta Baya Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: @bcrworldwide
Asali: Instagram

Sai dai kuma, a yayin daukar hoton, mai hoton ya aikata wani abu da sam bai yiwa angon dadi ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Ba Da Jimawa Ba, Gwamna Wike Ya Fallasa Wani Shiri

Don ganin hotunan sun kayatu sosai, mai hoton ya je kusa Da amaryar don yin tsayuwar daukar hoto da ita yayin da angon ke kallo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rike amaryar ta baya lamarin da bai yiwa angon dadi ba. Sai mijin ya kalle shi da bacin rai sannan ya ture shi daga wajen matarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu

Bcr_ tace:

"Wahala! Yana kokarin kwatanta abun da ya kamata angon yayi ne.”

Ms_jibbie ta rubuta:

“Allah ya so ka angon yana da sanyi, da wasu mutane ne da sun magareka.”

Meet_mimi_ ta yi martani:

"Oga photo, ka kwatanta da bakinka. Za mu ji kwatancin.”

Sammybigname50 ya ce:

“Menene ma’anar wannan.”

Tsoffin Maza Sun Fi Iya Soyayya: Matashiya Yar Shekaru 30 Da Ta Auri Dan Shekaru 80

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

A wani labarin, wata mata da ta dulmiya a cikin soyayya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan ta bayyana irin soyayyar da suke sha da sahibinta, wanda zai iya yin kaka da ita.

Matashiyar wacce ta fito da Mudaka, yankin Kudancin Kivu a damokradiyyar Kongo, ta ce soyayya babu ruwansa da banbancin shekaru kuma bai da iyaka.

Tsawon shekaru biyu kenan da Mwamini ta auri burin ranta Katembela Etienne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel