Bidiyon Wani Mutumin da Ya Sanya Takalmi Mai Siffar Kada Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Wani Mutumin da Ya Sanya Takalmi Mai Siffar Kada Ya Girgiza Intanet

  • Wani mutum ya girgiza zaman lafiyar intanet biyo bayan yada wani bidiyonsa a lokacin da yake sanye da wani nau'in takalmi
  • Takalmin dai ga shi nan ya siffanta da kada, ga hannaye da kafafu da komai na halittar kada a jikinsa
  • Jama'ar soshiyal midiya sun kasa kame bakinsu, da yawa sun tofa albarkacin baki kan wannan shiga mai ban mamaki

Caba ado da kwalisa abu ne na ra'ayi, kuma bai cika kawo cece-kuce ba, saboda an ce ra'ayi riga kuma kowa da kalar tasa.

Sai dai, wani ya girgiza ashafukan intanet yayin da yazo da wani sabon salo da ba a saba gani ba, inda ya sanya takalmin da ya jawo cece-kuce.

An ga faifan bidiyon lokacin da yake sanye da takalmi mai siffar kada, kama daga kafar dabbar har zuwa hannaye da gefenta.

Bidiyon mutumin da ya sanya takalmi mai siffar kada
Bidiyon wani mutumin da ya sanya takalmi mai siffar kada ya girgiza intanet | Hoto: @mediaroomhub
Asali: Instagram

Bakaken takalman sun nuna sak siffar dabbar da ke rayuwa a cikin ruwa, lamarin da yasa mutane ke ta'ajibin salonsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gani ya kori ji:

Jama'a sun yi martani

Bayan yada bidiyon ta Instagram, ga dai kadan daga abin da mutane ke cewa:

wasehembadoon:

"Lacoste na gaske kuma a zahiri kenan."

chinwe_oriaku:

"Kada ta gaske."

samuelotigba:

"Makurar Inyamuri kenan bayan rabuwa da rigar raga."

ujinrosean1:

"Ya kamata ya yi tafiya dasu mu gani mana."

officialibadanproperties:

"Idan dan uwa Inyamuri ya samu wannan takalmin."

favouredgracerealtor:

"Ta yaya za ka sanya wadannan kuma ka hade kafafunka duba da hannaye da kafafunsa."

Yadda Saurayi Ya Guji Budurwarsa Saboda Gano Ta Kama Sana’ar Siyar da Kifi

A wani labarin na daban, wata kyakkyawar budurwa ta shiga jerin bidiyon kalubale, inda ta bayyana dalili da yadda ta rabu da wani saurayinta da ya nuna zai i watsi da ita.

Da take bayani a TikTok, budurwar ta ce saurayin nata ya gudu ne saboda kawai ta fara sana'ar tallan kifi.

Budurwar ta ce sam ba a yin ta mutane a rayuwa, kuma kowa da irin abin da ya zabar ma kansa. Ta ce a yanzu dai ta habaka, domin ta kai ga gina kasuwancin kasa da kasa ta sanadiyyar siyar da kifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel