Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Sanar da Wani Mummunan Lamarin da ya Faru a Magarkamar Kuje

Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Sanar da Wani Mummunan Lamarin da ya Faru a Magarkamar Kuje

  • Hukumar gidajen gyaran hali ta najeriya reshen babban birnin tarayya ta sanar da mutuwar daya daga cikin mazauna gidan dake Kuje
  • Kamar yadda kakakin hukumar Chukwuedo Humphrey ya bayyana, ya rasu sakamakon rashin lafiyan da yayi fama da shi
  • Ya sanar da cewa, mutumin ya rasu a cikin kwanakin karshen mako kuma an garkame shi ne tun shekarar 2019

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar gidajen gyaran hali ta babban birnin tarayya, ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin mazauna gidan yarin Kuje, jaridar TheCable ta rahoto.

Kakakin hukumar na Abuja, Chuckwuedo Humphrey, yace mazaunin gidan yarin ya rasu ne sakamakon wani matsanancin ciwo kuma ya shiga gidan a shekarar 2019.

Magarkamar Kuje
Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Sanar da Wani Mummunan Lamarin da ya Faru a Magarkamar Kuje. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yace an sanya mamacin a karkashin kula ta musamman ta tawagar masana kiwon lafiya a magarkamar inda ake duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki

Humphrey yace a wasu lokutan an dinga kai mamacin asibitin koyarwa na jami'ar Abuja dake Gwagwalada idan bukatar hakan ta taso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Amma abun jimami, lokacin da rashin lafiyarsa ta ta'azzara a ranakun karshen mako, duk wani kokarin masana kiwon lafiya na ceto shi ya gagara," yace.
"An shirya taron addu'a na musamman wanda ma'aikata da 'yan gidan gyaran halin suka yi wa mamacin."

Humphrey yace Ahmed Musa, shugaban hukumar, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin tare da abokansa.

Yace shugaban hukumar yace ya mayar da hankali wurin saka lafiya da walwalar mazauna gidan kan sahun gaba

Ya shawarci masu matsalar rashin lafiya na musamman da su kasance masu kiyayewa umarnin kwarraru domin gujewa kalubalen rashin lafiya.

'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Niger tace bata kama wasu bakin haure a kasar nan suna rarraba makamai ta jirgin sama ga 'yan bindiga a jihar ba.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Matar Aure Da Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Monday Kurya ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna a ranar Juma'a cewa, lamarin bai taba faruwa ba kowanne sashi na jihar.

Kurya ya kwatanta rahoton da labarin bogi dake yawo a soshiyal midiya saboda bai taba faruwa a jihar ba, Daily Nigerian ta rahoto hakan.

"Ba mu kama wani 'dan kasar waje da helikwafta yana raba makamai ga 'yan bindiga ba yankin da muke kula da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel