Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki

Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki

  • Malaman jami'a a Najeriya zasu yi ganawar yanke shawara ko a cigaba da yaji ko kuma a janye
  • Gwamnatin tarayya ta ce ta biyawa ASUU wasu bukatunta kuma ya kamata yanzu su janye yajin
  • Majiya tace gwamnati ta yi barazanar haramta kungiyar ASUU idan basu koma aji ba

Majalisar zartaswar kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya watau ASUU a daren Lahadi zata zauna kan yanke shawara kan yajin aikin da aka kwashe watanni shida anayi yanzu.

Za’ayi kwana ana wannan zaman daga daren Lahadi zuwa Safiyar Litinin.

Majiyoyi sun bayyana cewa ga dukkan alamu Lakcarorin basu shirya da gwamnati ba kuma zasu cigaba da yajin aikin, rahotonVanguard.

Wani Mamban majalisar wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa shirye suke su saka wando daya da gwamnati.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

Yace,

"Ba bakon abu bane bararzanar da gwamnati keyi na soke kungiyarmu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A lokacin mulkin Soja an yi kuma mun tsira. Yakin gaskiya muke yi. Idan sashen Ilimi ya gyaru, dukkanmu zamu amfana. "
"Wadanda ke gwamnati basu damu sashen ilimi ya lalace ba saboda 'yayansu basu karatu a nan."
ASUU Stirke
Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki
Asali: UGC

Gwamnatin Tarayya Na Shawarar Soke Kungiyar ASUU Gaba Daya

Bayanai da aka samu sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya na shawarar haramta kungiyar ASUU idan mambobinta suka ki janyewa daga yajin aiki duk da tagomashin da ttayi musu.

ASUU ta lashi takobin cewa sai gwamnati ta biyasu kudin albashin watanni biyar da sukayi suna yajin aiki kafin su koma Aji.

Ita kuma gwamnatin tarayya tace ba zata biya wadannan kudade ba kamar yadda Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyanawa manema labarai ranar Alhamis.

Vanguard ta ruwaito cewa majiyoyi da dama daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa idan ASUU taki janyewa daga yajin, gwamnati zata yanke shawarar soke su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel