'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

  • Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta karyata labarin dake yawo na bakin haure dake rarrabawa 'yan bindiga makamai ta jirgin sama
  • Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Monday Kurya, ya bayyana, yace hakan bai taba faruwa ba kuma labaran bogi ne
  • Yayi kira ga mazauna jihar da su cigaba da basu goyon baya wurin ganin an dakile garkuwa da mutane, 'yan bindiga da satar shanu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Minna, Niger - Rundunar 'yan sandan jihar Niger tace bata kama wasu bakin haure a kasar nan suna rarraba makamai ta jirgin sama ga 'yan bindiga a jihar ba.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Monday Kurya ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna a ranar Juma'a cewa, lamarin bai taba faruwa ba kowanne sashi na jihar.

Kurya ya kwatanta rahoton da labarin bogi dake yawo a soshiyal midiya saboda bai taba faruwa a jihar ba, Daily Nigerian ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai

Jirgin Police
'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Ba mu kama wani 'dan kasar waje da helikwafta yana raba makamai ga 'yan bindiga ba yankin da muke kula da shi."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

yayi kira ga jama'a da su yi watsi da wannan rahoton kuma su goyi bayan 'yan sanda ta hanyar basu bayanai da zasu iya sa a cafke miyagu masu addabar al'umma a jihar.

”Abinda muke bukata daga jama'ar kirki shine bayanai masu amfani kan kai da kawowar miyagu, ballantana a yankunan kauyuka domin dakile annobar garkuwa da mutane, 'yan bindiga da satar shanu," yace.

Kwamishinan yace 'yan sanda zasu cigaba da mayar da hankali wurin ganin bayan makiyan al'umma domin tabbatar tsaro.

Kurya yayi kira ga 'yan kasa nagari da su kasance masu sanya ido tare da hanzarta kai rahoton duk abinda suka zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Matar Aure Da Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

Ya tabbatarwa da mazauna jihar da sy kasance masu sirranta dukkan inda suka samo bayanai.

'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai

A wani labari a daban, rundunar 'yan sandan jihar Legas tace ta cafke wasu sojan bogi biyu a jihar. Kakakin rundunar 'yan sandan, Benjamin Hundeyin, yace an same shi da kayan sojoji, 'yan sanda, layu da harsasai masu rai.

A wata takarda da ya fitar, Hundeyin yace Oluwatosin Gabriel, daya daga cikin wadanda ake zargin, ya shiga hannu ne yayin da ake dabbaka dokar haramcin yawon babura a wasu sassan jihar, TheCable ta rahoto.

Yace 'yan sanda suna binciken kwakwaf wanda hakan ya kai ga kama Nurudeen Agboola, wanda ake zargi na biyu wanda shi ke samar da kayan sojojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel