Ana Zargin Matar Aure Ta Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

Ana Zargin Matar Aure Ta Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

  • Ana zargin wata mata da kisan mijinta cikin dare daga ita sai shi a cikin gidan a jihar Kebbi
  • Makwabta sun gaggauta kiran yan sanda yayinda suka ji hayaniya na fitowa daga cikin gidan
  • An damketa kuma an kai lamarin ofishin CID don bincike mai zurfi kan gaskiyar abinda ya faru

Birnin Kebbi - Hukumar yan sandan jihar Kebbi ta damke wata matar aure kan zargin kashe tsohon mijinta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Juma'a a Birnin Kebbi, birnin jihar, rahoton DailyNigeria.

Ya ce sun damke matar ne daren Alhamis bayan samun labari daga wajen makwabta da suka ji ihu cikin dare.

Kara karanta wannan

Hamisu Wadume: An sake Sojojin Da Suka Kashe Yan Sanda, Har An Karawa Kyaftin Balarabe Girma

A cewar jawabin:

"A ranar 25 ga Agusta misalin karfe 11:40 na dare, jami'an yan sandan hedkwata Gwadan Gwaji sun samu labarin cewa an yi ihu daga gidan wani makwabci, Attahiru Ibrahim na Aliero quarters."
"Yayinda muka samu labari, da wuri aka tura jami'an tsaro gidan kuma suka balla kofar gidan."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun tarar da Ibrahim kwace a kasa jina-jina kuma daga baya Likita ya tabbatar da mutuwarsa.
"Hakazalika an ga Matarsa, Farida Abubuakar, cikin gidan."

Kakakin yan sanda yace matar ake zargi da kisan mijin kuma an garkameta.

Kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, ya bada umurnin mayar da lamarin ofishin CID don bincike mai zurfi.

Kebbi
Ana Zargin Matar Aure Ta Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa
Asali: UGC

Kotu Ta Umurci A Rataye Shararren Ɗan Damben Gargajiya Har Sai Ya Mutu Saboda Kashe Matarsa Da Duka

A wani labarin daban, wata kotu da ke Adamawa ta yanke wa wani dan dambe, Thank-You Grim, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe matarsa, Kwalla Grim a karamar hukumar Guyuk.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

Babban alkalin jihar Adamawa, Mai sharia Nathan Musa, ya yanke wa dan damben hukuncin kisa bayan kotu ta same shi da laifin kisar kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel