Minista Pantami Ya Samo Wa Mutanen Gombe Tallafin Abinci Daga Hannun Shugaba Buhari

Minista Pantami Ya Samo Wa Mutanen Gombe Tallafin Abinci Daga Hannun Shugaba Buhari

  • Ministan sadarwa na Naajeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi rabon kayayyakin abinci a jiharsa ta Gombe
  • Ya bayyana cewa, shi da kansa ya samo wannan tallafi daga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Ministan ya kai ziyara jihar Gombe a karshen mako, inda ya kaddamar da wasua ayyuka baya ga rabon abincin

Jihar Gombe - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana samo wa jama'ar Gombe tallafin kayan abinci daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ministan ya bayyana cewa, akalla buhunnan kayan abinci 8,228 ne ya raba a Gombe, inda aka ba da kayyakin ta hannun sarakunan gargajiya a jihar.

Pantami ya yi rabon abinci a jihar Gombe
Minista Pantami ya samo wa mutanen Gombe tallafin abinci daga hannun shugaba Buhari | Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Hakazalika, ya ce sauran wadanda suka wakilci jama'arsu wajen karbar kayayyakin malaman addini da sauran shugabannin al'umma.

Pantami ya yada hotunan yadda aka yi wannan rabo a jihar Gombe a jiya Asabar, 27 ga watan Agusta, kamar yadda ya yada a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Pantami ya yada hotuna tare da cewa:

"Kayan abinci buhu dubu takwas, da dari biyu da ashirin da takwas (8,228) wanda Ministan sadarwa, ya nemo wa mutanen Gombe cikin tallafin shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.
"Dukkan kayan abincin an raba shi ta hannuwan sarakuna, da Malaman addini da sauran shuwagabannin al'ummah."

Kalli hotunan yadda mutanen Gombe suka karbi kayayyakin abinci daga hannun Minista Pantami a kasa:

Hotuna: An Bude Katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe Ranar Juma’a

A wani labarin, an bude sabon katafaren Masallacin Juma'a a garin Kaltungo dake karamar hukumar Kaltungo dake jihar Gombe. An kaddamar da wannan babban Masallacin ne ranar Juma'a, 26 ga watan Agusta, 2022.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya; tsohon gwamnan jihar Bauchi na mulkin soja, Alhaji Rasheed Adisa Raji; Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

Hakazalika akwai Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar bn Umar bn Amin Elkaneni, da A chikin mahalarta taron akwai, Mai martaba Sarkin Dutse, Mai martaba Mai Fika, Mai martaba Sarkin Dukku, Mai martaba Sarkin Deba, Mai martaba Sarkin Shani, Mai martaba Sarkin Gaya, Mai martaba Polo Dadiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.