Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

  • Daya daga cikin matan Sheikh Goni Aisami ta bayyana halin da suka shiga sakamakon mutuwar babban malamin
  • 'Dansa dake karatu a jami'a ya bayyana maganarsa ta karshe da yayi da mahaifinsa ana gobe mutuwarsa
  • Hukumar yan sanda ta ce nan ba da dadewa ba zata gurfanar da Sojojin da suka kashe Malamin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Uwargidar Marigayi, Sheik Goni Aisami, Mallama Aisha ta bayyana maganarta ta karshe da tayi da babban Malamin yayinda yake hanya gab da ya dauki Sojan da yayi ajalinsa.

Mallama Aisha, wacce daya ce daga cikin matan Sheikh Aisami, ta ce wannan mumunan kisa da akayiwa maigidanta ya canza rayuwarsu gaba daya kuma an cucesu har abada, rahoton BBC.

A cewarta,

"Na kirashi sau uku bai dauka ba, sai daga baya ya kira cewa yana hanya har ya fadawa dan yaronsa mai shekara hudu cewa ya sayo masa burodi da Bobo."

Kara karanta wannan

'Ba Zamu Zuba Ido Ba' Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki Kan Batun Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

"Wannan makashin ya cucemu har abada, ba zamu taba mantawa ba."
Iyalan Aisami
Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami Hoto: www.bbc.com/pidgin/articles
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daya daga cikin 'yayan babban Malamin wanda ke aji biyu a jami'a, Abdullahi Goni Aisami, ya bayyana cewa yana da kanne takwas wadanda ke karatun firamare da sakandare.

Yace ranar Alhamis yayi maganar da mahaifin kawai sai ya samu labarin mutuwarsa ranar Juma'a.

A cewarsa:

"Muna zana jarabawa ne a makaranta abin ya faru. Na yi magana da shi da yammacin Alhamis har ya fada min ya turo min wasu kudi ashe karshen maganarmu kenan."

Abdullahi ya tabbatar da labarin cewa gwamnatin jihar Yobe ta baiwa babban yayansa aiki bayan abinda ya faru.

Abinda Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Yayinda Na Daga Bindiga Zan Harbesa: Barawon Soja

Lance Kofur John Gabriel ya bayyana yadda ya yaudari Sheik Goni Aisami-Gashua, kafin harbinsa da bindiga har lahira a kan titin Gashua- Jaja Maji.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata

Yayinda jawabi lokacin da yan sanda suka gabatar da shi gaban yan jarida ranar Laraba, Kofur John ya ce babban Malamin ya yi masa tambayoyi biyu yayinda yake kokarin kashe shi.

Karanta cikakken Labarin anan

Asali: Legit.ng

Online view pixel