Bidiyon Shigowar Kasaita da Iyalan Bayero Suka yi Wurin Liyafar Auren Kabiru Aminu Bayero

Bidiyon Shigowar Kasaita da Iyalan Bayero Suka yi Wurin Liyafar Auren Kabiru Aminu Bayero

  • Shigar iyalan Bayero wurin liyafar cin abincin dare ta auren Kabiru Aminu Bayero ta matukar daukar hankali
  • An ga kyawawan 'yan matan sun yi shigar koren kaya yayin da mazan suka sanya manyan riguna da hulun cikin kasaita
  • Ana cigaba da shagalin auren ango Kabiru Aminu Bayero da dalleliyar amaryarsa Aisha Ummaru Kwabo a Sokoto

Sokoto - Ana cigaba da shagalin auren Kabiru Aminu Ado Bayero da kyakyawar amaryarsa Aisha Ummarun Kwabo a garin Sokoto.

Tun daga fara shagalin bikin garin Sokoto ya dauka 'yan uwa, masoya da abokan arzikin ango Kabiru Aminu Bayero da amaryarsa Aisha Ummaru Kwabo.

Bayero
Bidiyon Shigowar Kasaita da Iyalan Bayero Suka yi Wurin Liyafar Auren Kabiru Aminu Bayero. Hoto daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Bayan shagalin kamun amarya Aisha da aka yi a daren Laraba, daren Alhamis an yi liyafar cin abincin dare inda aka ga kwai da kwarkwatar iyalan Bayero a wurin kasaitacciyar liyafar.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Wani abu da ya matukar daukar hankali shi ne yadda jinin sarautar suka shiga wurin liyafar cikin kasaita da kwalisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga wasu daga cikin 'yan matan sun yi shiga kaya mai launin kore amma mai haske inda suka sanya kallabi mai launin kore mai duhu, lamarin da ya fito da hasken fatarsu karar.

A cikin mazan gidan sarautar kuwa, duk sun bayyana ne sanye da shadda mai kyau wacce aka yi musu dinkin babbar riga sannan suka biye ta da huluna 'yan zamani.

Bidiyon da @arewafamilyweddings suka wallafa a shafinsu na Instagram ya bayyana har da sirikar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero a wurin liyafar cikin shigar alfarma.

Kyawawan Hotuna da Bidiyo Daga Kamun Kabiru Aminu Bayero da Tsuleliyar Amaryarsa

A wani labari na daban, kyawawan hotuna da bidiyoyin wurin kamun ango Kabiru Aminu Bayero da zukekiyar amaryarsa, Aisha Ummarun Kwabo sun matukar kayatar da jama'a.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

Biki tuni dai ya kankama inda ake hango ranar daurin aure, Juma'a, 26 ga watan Augustan 2020 a jihar Sokoto.

A daren Laraba ne aka fara da shagalin bikin auren inda kamun da aka yi ya matukar kayatarwa ganin yadda kyakyawar amaryar ta fito shar cikin shiga ta alfarma da kwalisa.

A hotuna da bidiyoyin da @faashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga ango Kabiru Aminu Bayero sanye da shigar manyan mutane kuma ta alfarma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel