Ta Yaya Ta Iso Nan? An Gano Yarinya Yar Shekara 17 Da Ta Bace A Legas A Jihar Arewa
- Yarinya yar shekara 17 mai suna Mildred Ebuka wacce ta bace a Legas ta bayyana a Jihar Bauchi
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil ya ce a tashar mota aka gano ta tana barci
- Wakil ya ce wata mata ta gano ta tana barci a tashan mota kuma bayan ta tashi ba ta iya tuna yadda aka yi ta iso Bauchi ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bauchi - Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tsinci wata yar shekara 17, Mildred Ebuka, wacce ta bace a ranar Alhamis yayin komawa gida bayan an tura ta kai sako a Legas, The Punch ta rahoto.
An rahoto cewa Ebuka ta bar gidansu ne a Victoria Island a ranar Alhamis domin kaiwa kawar gwagwanta gashi a Ikorodu Legas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar yan sandan na Jihar Bauchi ta sanar da al'umma cewa yarinyar tana hannun ta.
A sanarwar da ta fitar ta shafinta na Twitter, rundunar yan sandan ta ce:
"Mildred Joshua Ebuka mace yar shekara 17 mai zaune a Block 19 Ubandale street Victoria Island Legas, wanda hotonta ke kasa ta bar gida ranar Alhamis 25/08/2022 don kai wa kawar gagwanta sako a Ikorodu, a hanya ta tsayar da tasi kusa da gida daga nan ta tsinci kanta a Bauchi.
"Yar asalin jihar Legas ne kuma tana magana da harshen turanci. Tana sanye da riga mai launin bula da wanda, fara ce kuma bata da zane."
Kakakin yan sandan Bauchi ya ce a tashar mota aka tsince ta
SP Ahmed Wakil, mai magana da yawun rundunar yan sandan Bauchi ya shaidawa Punch a ranar Juma'a cewa an tsinci Mildred ne a tashar mota a Bauchi.
Wakil ya ce:
"An fitar da sanarwar ne don a gano iyayenta. Ba ta iya tuna komai ba lokacin da ta iso Bauchi. Wata mata ta tashe ta a tasha, kuma bata san inda ta ke ba.
"Don haka, aka tuntubi yan sanda, kuma ofishin hulda da jama'a ta sanar da ni. Shi yasa na fitar da sanarwa."
Kakakin yan sandan Jihar Legas ya yi martani
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ya ce an bincika amma ba a gano wannan adireshin ba.
Ya ce:
"Muna fata yan uwanta za su tuntube mu idan sun ga hotonta."
Asali: Legit.ng