Matashi Mai Shekaru 25 ya Make Matar Babansa da Tabarya, Ya Bayyana Dalilinsa

Matashi Mai Shekaru 25 ya Make Matar Babansa da Tabarya, Ya Bayyana Dalilinsa

  • Rundunar 'yan sandan jihjar Katsina ta damke matashi mai suna Najib Shehu mai shekaru 25 a duniya
  • Matashin ya ragargaje matar babansa da tabarya ne wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta har lahira
  • Sai dai matashin ya bayyana cewa, bai aikata lamarin ba kare kansa ya je yi amma tabaryar ta make ta a kai inda ta fadi matatta

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis tace ta kama matashi mai shekaru 25 mai suna Najib Shehu wanda yayi amfani da tabarya wurin halaka matar babansa.

Kamar yadda rundunar 'yan sandan tace, lamarin ya faru a ranar Alhamis da ta gabata kuma a kowanne lokaci za a iya gurfanar da shi a gaban kotu.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan jim kadan bayan kama Shehu a hedkwatar rundunar a Katsina. An bayyana shi tare da tabaryar da yayi amfani da ita wurin halaka matar mai shekaru 60.

Kara karanta wannan

Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

Wanda ake zargi
Matashi Mai Shekaru 25 ya Halaka Matar Babansa, Ya Bayyana Dalilinsa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Shehu wanda yayi magana da harshen Hausa yayi bayanin cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sunana Najib Shehu. Shekaruna 25 kuma ina aji biyu a jami'ar tarayya ta Dutsina-ma.
“Ina ta samun matsaloli da matar babana. Amma a ranar Alhamis, na idar da sallah sai na dawo gidanmu. Mahaifina yana zaune a dakinsa sai matar babana ta shigo rike da tabarya tana yi min barazana.
"Ta daga tabaryar ta buga min a goshi amma sai na kare. Daga nan sai ta so buga min kafa amma kasancewata 'dan kwallo, na daka tsalle tare da tsallakewa. Wannan sai ya buga kafar mahaifina wanda ya zo kawo dauki.
"Matar babana ta sake daga tabaryar tana son buga min a kai amma na tureta, a hakan tabaryar ta buge ta a kai kuma ta fadi ta mutu.
"Mahaifiyata ita ce matar farko kuma sun rabu da mahaifina. Ina zama ne da babana tare da matarsa a kwatas din ambasada dake Katsina. Nayi nadamar abinda nayi duk da ban so aikatawa ba."

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotuna da Bidiyo Daga Kamun Kabiru Aminu Bayero da Zukekiyar Amaryarsa Aisha

Punch ta rahoto cewa, kakakin rundunar ya sanar da manema labarai cewa za a gurfanar da Shehu a kotu ana kammala bincike daga wurin 'yan sanda.

Zamfara: Kwamitin Yakar 'Yan Bindiga Ya Gindaya wa Turji Sharadin Tuba

A wani labari na daban, Kwamitin jihar Zamfara na gurfanar da laifukan da suka shafi 'yan bindiga sun ce har sai Bello Turji, fitaccen shugaban 'yan bindiga ya fito bainar jama'a ya mika makamansa tare da sanar da tubansa, ba za a karba tubansa a matsayin sahihiya ba.

Shugaban kwamitin, Abdullahi Shinkafi, ya sanar da hakan a jawabin da yayi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.

Shinkafi wanda ya fito daga karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda Turji ke yawaita barnarsa, yace kusan watanni shida kenan babu labarin farmakin 'yan ta'adda ko sace mutane da aka saba a yankin da kananan hukumomin Zurmi, Isa da Sabon-Birni.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sheke Babban Sojan Najeriya a jihar Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel