An Kama Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Borno Zata Tafi Da Su Legas

An Kama Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Borno Zata Tafi Da Su Legas

  • Dubun wata mata ya cika yayinda aka damketa ta sace yaran mutane a Borno zata tafi da su Legas
  • Matar tace kwangila aka bata na kudi dubu dari biyar (N500,000) don aikata wannan aika-aika
  • Wannan na shine karon farko da wasu ke zuwa Arewa daga Kudu don satan yara da sayar da su

Borno - Hukumar yan sanda a jihar Borno ta bayyana wata mata mai shekara 46, Insa Henshaw, ranar Alhamis, 25 ga Agusta kan laifin satar yara uku zata gudu da su jihar Legas.

An damke matar ne a tashar mota, rahoton HumAngle.

A cewar yan sanda, an damketa ne makonni uku da suka gabata lokacin da aka ganta tana kokarin hawa motar da yaran.

Kara karanta wannan

Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

Hukumar tace mutane a tashan ne suka lura ba tada natsuwa sai suka kira yan sanda.

Yara 3
An Kama Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Borno Zata Tafi Da Su Legas Hoto: Abdulkareem/HumAngle
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishanan yan sandan jihar, Abdu Umar, ya sanar da manema labarai cewa an sameta da kudi N400,000 a hannu.

Yace:

"Mrs Insa Henshaw yar shekara 46 wacce tsakanin ranar 5 da 6 ga Agusta ta sace yara uku Mustapha Abdullahi, 7, Abdullahi Mustapha, 5, and Hajara Alhassan, 3, da niyyar kaiwa wata mata mai suna Lady-B wacce ta bata kwangilan N500,000."
"An kama ta da kudi N410,000 daga cikin kudi kuma an kwace."

Ya kara da cewa an kwace yaran daga hannunta suna cikin koshin lafiya kuma an mayar da su wajen iyayensu.

Matar tace bayyanawa yan sanda cewa wata mata a Legas ce ta asirceta wanda hakan ya tunzurota jihar Borno satan yara.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ‘Yan fanshi da Barayi Sun sace Wayoyi 76 da Kayan kusan N5m

Wata Mata Ta Sayar Da Jaririn Da Ta Haifa Mako Uku N600,000 a Ogun

A wani labarin kuwa, jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Ogun sun kama wata mata ƴar shekara 23, Mary Olatayo, bisa zargin ta sayar da jariri ɗan mako uku kan kuɗi N600,000.

Daily Trust ra rahoto cewa wacce ake zargin ta shiga hannu ne bayan mahaifin jaririn ya shigar da ƙorafi a Ofishin yan sanda dake Mowe, ƙaramar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun.

Kakakin hukumar yan sanda, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abeokuta ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel