Cunkus Dakin Tsumma: Fusataccen Mazaunin Lagas Ya Hadu Da Cunkoso A Teku, Bidiyon Ya Yadu

Cunkus Dakin Tsumma: Fusataccen Mazaunin Lagas Ya Hadu Da Cunkoso A Teku, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani dan Najeriya ya ziyarci yankin Makoko da ke jihar Lagas kwanan nan sannan ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda wurin ya kacame
  • Yayin da yake daukar bidiyon yadda yankin yake matashin ya yi korafi sosai game da yadda ake samun cunkoso a Lagas har a Teku
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun nuna rashin jin dadinsu yayin da mutane da dama suka yi kira ga gwamnatin jihar a kan ta yi wani abu game da cunkoso

Lagas - Tsawon shekaru da dama mazauna jihar Lagas na korafi game da yawan cunkoson ababen hawa a jihar.

Matafiya sun ce wasu lokutan su kan shafe tsawon awanni a cunkoson ababen hawa kan tafiyar da bai kamata ace ya wuce minti 30 ba.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Tinubu ya fadi sana'ar da yake ya tara makudan biliyoyi

Cunkoso
Lagas Cunkus Dakin Tsumma: Fusataccen Mazaunin Lagas Ya Hadu Da Cunkoso A Teku, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @gossipmilltv / Alvarez
Asali: Instagram

Yayin da korafin ya fi yawa a kan zirga-zirgan haya, wani matashi a cikin wani bidiyo da ya yadu, ya bayyana cewa lamarin ya kai har ga yankunan teku.

Ya wallafa bidiyonsa a Makoko, wani gari a jihar Lagas, kuma bidiyon ya nuna yadda aka samu cunkoson mutane a cikin jiragen ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi martani masu yawan gaske kan bidiyon yayin da yan Najeriya suka bayyana ra’ayoyinsu game da yadda mutane ke rayuwar bakin ciki a wannan yankin.

Yan Najeriya sun yi korafi a kan cunkoson ababen hawa a Lagas

Mc_mrpope ya ce:

“Allah ya kawo agaji.”

Muyee_wazy ya bayyana:

“Allah ya kyauta. Har a cikin teku ake cunkoso. Lagas Allah ya kyauta.”

Amarachi_gabriella ta rubuta:

“Allah. Ban taba ganin wuri irin haka ba.”

Khalifa_officiall ya yi martani:

“Har a kan teku cunkoson ababen hawa na kama mutum.”

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali

Legit.ng ta zanta da wasu mazauna Lagas don jin yadda suke fama da wannan matsala ta cunkoson ababen hawa inda kowannensu ya nuna damuwa ainun kan haka.

Alhaji Kabiru Abdullahi wani mazaunin Agege ya ce wannan matsala ta zama kamar wani bangare na rayuwar duk wani mazaunan jihar yana mai cewa:

“Gaskiya kamar ni a yanzu na saba da wannan abu iyakaci kawai na kan tsara yadda zan tafiyar da harkokina ba tare da lokaci ya kure mun ba. Misali na kan shiga kasuwar Balogun siyayya, toh abun da na kan yi da asubahi nake tafiya ana sallamewa, sai ki ga na isa a kan lokaci. Kuma duk rintsi bana yarda 3:30 na rana ya yi mun a kasuwa saboda a lokacin ne ake fara samun go-slow ma’aikata sun fara tashi daga aiki.”

A nashi bangaren Salisu Shu’aibu ya ce shi har yak an shiga zullumi idan aka ce wani abu zai kai shi cikin gari.

Kara karanta wannan

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

“Ai ni har bana fatan tafiya mai nisa da sai an shiga mota ta ritsa dani. Tafiya idan nisan ta ya wuce Ikeja bana kaunarta. Don ainahin cunkoson a cikin gari yake. Ni ina ganin mawuyacin abu ne ma ace za a iya magance wannan matsala ta cunkoso a Lagas. Mu mazauna cikinta har mun saba kawai dai wasu lokutan ne abun akwai cin rai.”

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

A wani labarin, mun ji cewa tsarin cikin wani jirgin sama ya haifar da martani masu yawan gaske a Instagram bayan an dauki bidiyonsa tare da yada shi a dandalin na soshiyal midiya.

A cikin dan gajeren bidiyon mai numfashi, an hasko yadda aka kawata cikin jirgin gaba dayansa kuma hakan ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu.

Jirgin saman mai zaman kansa na dauke da manyan dukanan barci guda biyu da wasu wuraren zama da suka yi kama da kananan dakunan taro.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng