Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali

Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali

  • Wata kyakkyawar mata ta haifi yan hudu bayan shafe shekaru bakwai tana jiran tsammani
  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno ma’aikatan asibiti suna fito da kyawawan yaran daga dakin karbar haihuwa
  • An yiwa yaran ado sannan aka shayar da su a cikin wani bidiyo wanda ya burge zukata da dama a yanar gizo

Allah ya albarkaci wasu ma’aurata da haihuwar kyawawan yara hudu a lokaci daya. A cikin bidiyon da ya bayyana a soshiyal midiya, yaran sun hadu matuka yayin da malaman asibiyi suka kula da su.

@bcrworldwide wanda ya wallafa bidiyon a Instagram ya bayyana cewa mahaifiyar yaran ta haife su ne bayan shekaru biyar tana jiran tsammani ba tare da samun haihuwa ba.

Yan hudu
Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali Hoto: @bcrworldwide
Asali: Instagram

Bidiyon ya burge mutane da dama a soshiyal midiya. Yayin da wasu mata da dama suka yi fatan samun yan biyu, wasu sun cika da farin cikin ganin wadannan kyawawan yara har guda hudu.

“Wannan abu da ya yi kyau matuka bayan shekaru 7 tana jira, ta roki Allah ya bata yan biyu amma ya albarkace ta da yan hudu. Ina taya ki murna,” Bcrwordlwide ya rubuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon kyawawan yan hudun ya tsuma zukata

Hada__design ta ce:

“Zan rera wannan wakar kwanan nan da taka sabon rawa a gaban Ubangijina.”

Gladyeraga ta rubuta:

“Kai! Allah gwanin kyauta ne ina taya ki murna ina fatan samun irin wannan tabarrakin.”

Adrianaowusuansah ta yi martani:

“Wannan shine Ubangijin da muke bautawa, Shine Allah mai sha yanzu magani yanzu.”

Browniej89 ta yi martani:

“Na taya ki murna. Ina fatan samun irin wannan tabarrakin.”

Kalli bidiyon a kasa:

Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

A wani labarin, hotunan girman cikin wata yar Najeriya mai dauke da juna biyu ya haifar da martani daga mutane a soshiyal midiya.

Yan shekaru da suka gabata, kyakkyawar matar ta haifi yara yan hudu wadanda aka sanyawa suna Camille, Casper, Carissa, da Casen.

Sunanta ya sha bayyana a kanen labarai bayan ta wallafa kyawawan bidiyoyin yaranta su hudu, kuma wasu mutane sun roki alfarmar ganin hotunta dauke da cikin yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel