Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

  • Wani hadadden bidiyo ya nuno cikin wani katafaren jirgin sama mai zaman kansa wanda ya ja hankula sosai a Instagram
  • Baya ga kyawu da haduwar ciki da wajen jirgin yana da manyan dakunan barci guda biyu a cikinsa
  • Kyakkyawan bidiyon jirgin ya haifar da cece-kuce a Instagram yayin da mutane suka kira shi da katafaren gida mai tashi sama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsarin cikin wani jirgin sama ya haifar da martani masu yawan gaske a Instagram bayan an dauki bidiyonsa tare da yada shi a dandalin na soshiyal midiya.

A cikin dan gajeren bidiyon mai numfashi, an hasko yadda aka kawata cikin jirgin gaba dayansa kuma hakan ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu.

Jirgin sama
Duniyar Sama: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya Hoto: @insanejets.
Asali: Instagram

Jirgin saman mai zaman kansa na dauke da manyan dukanan barci guda biyu da wasu wuraren zama da suka yi kama da kananan dakunan taro.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali

Bayan an wallafa bidiyon, ya burge masu amfani da soshiyal midiya yayin da suka tafi sashin sharhi don bayyana ra’ayoyinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Masu amfani da Instagram sun bayyana abun da za su yi ko wuraren da za su je a wannan jirgi idan aka basu dama. Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:

@jgw_main ya ce:

“Zan Lula Sydney, Australia daga wajen birnin New York ko kuma tafiya mafi tsawo don na more sosai sannan na nutsar da kaina cikin gogewa.”

@boop14 ya yi martani:

“Kawai mun mallaki wani dan karamin jirgi amma yana da kujerun zama tara amma muna da dan kushin da mutum uku za su iya zama ko a mayar da shi gado don barci.”

@kuunnall._ sya ce:

"Kira shi gida mai tashi sama.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa

@thursday___aug25_2022 ta yi martani:

“Ina tsoron fadin inda za ni.”

Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30

A wani labarin, kyawawan hotunan adaidaita sahu masu aiki da lantarki wanda kamfanin Phoenix Renewable Limited ya kera a Maiduguri sun yadu a shafukan soshiyal midiya.

Hadaddun hotunan adaidaita sahun wanda ake yiwa lakabi da Keke Napep ya sanya yan Najeriya da dama tofa albarkacin bakunansu sannan sun bukaci gwamnati da ta tallafawa kamfanin.

Shugaban kamfanin da ya kera adaidaita sahun, Mustapha Gajibo ya shahara wajen yin ababen hawa masu aiki da lantarki wanda yawancinsu motocin bas-bas ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel