Daga Karshe, Shettima Ya Magantu Kan Salon Shigar Da Ya Yi Zuwa Taron NBA

Daga Karshe, Shettima Ya Magantu Kan Salon Shigar Da Ya Yi Zuwa Taron NBA

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima ya yi karin haske kan salon shigarsa zuwa taron NBA a Legas
  • Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce da gangan ya saka takalman motsi jiki wato sneakers da kwat don kule wasu masu shirya masa makirci
  • Shettima ya yi ikirarin cewa masu masa leken asiri sun gano cewa tawagar wani dan takarar shugaban kasa sun shafe kwana uku sun kulla masa makirci kafin taron

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya magantu kan cece-kuce da aka rika yi kan salon shigar da ya yi zuwa taron NBA a ranar Litinin.

Shettima, wanda ya wakilci Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya dauki hankulan mutane a dandalin sada zumunta bayan daya cikin hotunansa a taron ya bazu.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

Shettima a NBA
Daga Karshe, Shettima Ya Magantu Kan Salon Shigar Da Ya Yi Zuwa Taron NBA. Hoto: Greenbrepoters.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi zarge tsohon gwamnan na Borno da rashin iya saka tufafi.

Masu fada a ji a dandalin sada zumunta da sauran mutane sun rika daukan hotunansu suna wallafawa don kwaikwayon shigar Shettima.

Martanin Shettima

Amma, da ya ke magana kan lamarin, Shettima ya ce da gangan ya saka takalmar motsa jikin wato 'sneakers', Daily Trust ta rahoto.

Ya yi zargin cewa wani dan takarar shugaban kasa, wanda bai bayyana sunansa ba, ya shirya masa makirci gabanin taron kamar yadda Nigerian Voice ta rahoto.

A cikin wani bidiyo, Shettima ya ce:

"Na tafi Legas don taron NBA. Ana taron na a Eko Hotels. Gwamnatin Jihar Legas ta APC ne galibi ke daukan nauyin taron. Daga baya, suka maya da taron zuwa Eko Atlantic City, shawara da ta fito daga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

"Da na aika yan leken asiri na, an gano cewa tawagar daya cikin yan takarar shugaban kasa sunyi kwana uku suna taro don kulla makirci. An fada min ba son mu ake a wurin ba ... Ni ma'aikacin banki ne, daya cikin ma'aikatan banki da suka fi kwarewa a duniya ya koyar da ni. Ni yaron Jim Ovia ne. Na gangan na saka takalman motsa jiki zuwa taron NBA don in 'watsa musu kasa a ido'."

Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a

Tunda farko, kun ji cewa Kashim Shettima, 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya janyo cece-kuce sakamakon shigar da yayi zuwa taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya na wannan shekarar.

A ranar Litinin, tsohon gwamnan jihar Bornon ya wakilci Bola Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a taron NBA da aakayi a Eko Atlantic City daga ranar 22 ga watan Agusta zuwa 26.

Asali: Legit.ng

Online view pixel