Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

  • Idan jam’iyyar APC ta yi nasarar cigaba da mulki a Najeriya bayan 2023, Kashim Shettima zai zama mataimakin shugaban kasar nan
  • Sanata Kashim Shettima ya shaida cewa shi zai kula da abin da ya shafi harkar tsaro, yayin da Bola Tinubu zai bunkasa tattalin arziki
  • ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar yayi shekara da shekaru yana fama da rikicin ‘Yan Boko Haram a lokacin da yake Gwamna

Lagos - Kashim Shettima wanda shi ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC, yace zai maida hankali ga tsaro idan suka kafa gwamnati.

Premium Times tace Sanata Kashim Shettima ya sha alwashin idan suka yi nasara a zaben 2023, zai kula da sha’anin tsaro domin kawo zaman lafiya.

Tsohon gwamnan na Borno ya bayyana wannan a wajen babban taron NBA na kasa da aka yi a Legas, inda ya gabatar da jawabi a gaban Lauyoyi.

Shettima ya fadawa mahalarta zaman da aka yi a farkon makon nan cewa jagoranci jami’an tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.

A gefe guda kuma, Bola Tinubu kamar yadda aka san yayi kokari wajen kawo cigaba a jihar Legas, zai dage wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

Abin da Shettima ya fada

“Na yi shekaru 18 a tsakiyar yaki, zan jagoranci jami’an tsaro, maigidana masanin tattalin arziki ne wanda ya gyara Legas, ta zama (cibiyar tattalin arziki) ta uku a Afrika."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kashim Shettima
Kashim Shettima a Legas Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shi (Tinubu) zai maida hankali a tattalin arziki. Da yardar Ubangiji, zan kula da tsaro, ba iyaka tsaro kurum ba, zan jagoranci sojoji zuwa ko ina a kasar.”

Karambani ko alkawari?

Jaridar tace wasu na ganin Shettima ya yi azarbabi da wadannan kalamai da yayi a bainar jama’a, domin ya shiga hurumin Mai girma shugaban kasa.

Sashe na 130 (2) na kundin tsarin mulki ya ba shugaban Najeriya ikon juya jami’an tsaro. Ko APC ta lashe zabe, Shettima ba zai samu wannan dama ba.

Chukwunomso Ogbe wanda masani kuma lauya ne, yace mataimakin shugaban kasa bai da wani hurumi a doka, sai aikin da shugaban kasa ya ba shi.

Martanin Atiku Abubakar

Da aka tuntubi Daniel Bwala, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, yace Sanatan yana fadan abin da ya fi karfinsa.

A matsayinsa na gwamnan Borno a 2013, Bwala yace Sanata Shettima ya yi sakaci a lokacin da aka sace ‘yan matan Chibok duk da an ankarar da shi.

Babu rigima da Wike - Atiku

Kun ji yadda aka hadu a Kasar waje dazu domin dinke barakar da ake tunanin ana samu tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike a tafiyar jam’iyyar PDP

A wani jawabi da aka fitar, ‘Dan takaran shugaban kasar ya gargadi mutane da su yi hattara da baram-baramar da za ta iya jawo a fadi zaben da za ayi a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel