Hotunan Masallacin Da Wani Ɗan Bautan Ƙasa Kirista Ya Gina Wurin Alwala Da Gyaran Bandaki A Zamfara

Hotunan Masallacin Da Wani Ɗan Bautan Ƙasa Kirista Ya Gina Wurin Alwala Da Gyaran Bandaki A Zamfara

  • Wani dan bautan kasa mai suna Jeremiah Shimasaan ya gina wurin alwala tare da gyaran bandaki gudu uku a masallaci a Zamfara
  • Jeremiah ya ce ya yi wannan aikin ne domin karfafa fahimta, zumunci da hadin kai tsakanin mabiya addinai a Najeriya da kuma saukakawa masu sallah a masallacin
  • Ahmad Liman, Sakataren dindindin na ma'aikatan muhalli na Jihar Zamfara yayin kaddamar da ayyukan ya yaba wa Jeremiah ya kuma yi kira da sauran su yi koyi da shi

Zamfara - Wani dan bautan kasa kirista, Jeremiah Shimasaan, da ke aikinsa a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ya gina wurin alwala kuma ya gyara bandaki guda uku a wani masallaci.

Ya kuma saka akwatin saka takardun bada shawarwari a kofar shiga ginin ma'aikatan gidajen rediyo da talabijin na Jihar Zamfara, Channels TV ta rahoto.

Dan NYSC A Zamfara
Zamfara: Dan Bautan Kasa Kirista Ya Gina Wurin Alwala Da Gyara Bandaki A Masallaci. Hoto: @ChannelsTelevision.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shimasaan, wanda ke aikinsa a gidan rediyo da talabijin na jihar Zamfara ya ce ya yi wannan aikin ne domin karfafa zumunci tsakanin mabiya mabanbantan addinai a Najeriya.

Dan NYSC a Zamfara
Zamfara: Dan Bautan Kasa Kirista Ya Gina Wurin Alwala Da Gyara Bandaki A Masallaci. Hoto: @ChannelsTelevision.
Asali: Twitter

Ya kuma ce ya gina wurin alwalan ne don saukaka wa masallata wahalan zuwa neman ruwan alwala da neman wurin yin tsarki kafin su yi sallah.

Kalamansa:

"Na yi wannan aikin a masallacin ne domin karfafa zumunci, hadin kai da zaman tare tsakanin mutane masu addinai daban.
Idan dukkan mu a kasar za mu rika mutunta addinin juna, kuma mu kaunaci juna, za mu samu irin Najeriyan da muke mafarkin samu ba tare da fada ko kashe juna ba."

Sakataren Dindindin Na Ma'aikatan Muhalli Ya Kaddamar Da Aikin

Ahmad Liman, Sakataren dindindin na ma'aikatan muhalli na Jihar Zamfara, ya yaba wa dan bautan kasar yayin kaddamar da ayyukan.

Barista Liman ya ce samun irin mutane kamar Jerry Shimasaan masu farar aniya na da wahala, amma Zamfara ta yi sa'an samunsa.

Ya ce aikin gina wurin alwalan da gyaran bandaki da ya yi zai sama sanadin albarka a rayuwarsa.

NYSC a Zamfara.
Zamfara: Dan Bautan Kasa Kirista Ya Gina Wurin Alwala Da Gyara Bandaki A Masallaci. @ChannelsTelevision.
Asali: Twitter

Sakataren ya bukaci sauran masu bautan kasa su yi koyi da abin da Shimasaan ya yi, yana mai cewa hakan zai taimaka wurin kawo zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Jeremiah Shimasaan ya yi digiri a bangaren Turanci da Adabi ne a Jami'ar Jihar Benue da ke Makurdi.

Sauran wadanda suka hallarci taron kaddamar da aikin sun hada da shugabannin NYSC, yan bautan kasa, shugabannin addini da wakilan unguwa da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel