FEC: Osinbajo Ya Bayyana a Aso Rock a Karon Farko Tun Bayan Yi Masa Aiki a Kafa

FEC: Osinbajo Ya Bayyana a Aso Rock a Karon Farko Tun Bayan Yi Masa Aiki a Kafa

  • Kamar yadda aka saba a duk Laraba, Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa na kasa a fadar Aso Rock
  • A taron makon nan, an ga bakuwar fuska a fadar shugaban kasa, domin Yemi Osinbajo ya samu halartar zaman na FEC a jiya
  • An shafe fiye da wata guda Mataimakin shugaban kasar bai je taron ba saboda aiki da aka yi masa a kafa a wani asibiti a Legas

Abuja - A ranar Laraba, 24 ga watan Agusta 2022, Mai girma Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar FEC wanda ake yi a fadar shugaban kasa.

Rahoton da gidan talabijin na Channels ya fitar a jiyan ya nuna wannan ne karon farko da aka ga Yemi Osinbajo a taron bayan daukar tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

A tsakiyar watan Yulin 2022 aka yi wa Farfesa Yemi Osinbajo aiki bayan samun matsala a kafa, ba a sallame shi daga asibiti ba sai bayan kwanaki.

Tun wancan lokaci, mataimakin shugaban kasar yana aiki ne ta yanar gizo daga gidansa. Sai jiya ya wartsake sosai, ya fara taka kafafunsa da kyau.

A makon nan Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Ministocin tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati suka yi ido hudu da Osinbajo.

Su wanene suka je taron FEC?

Leadership tace wadanda aka yi taron FEC da su a makon nan sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa da NSA, Janar Babagana Monguno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osinbajo
Ministoci da Osinbajo a taron FEC Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Akwai shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Folasade Yemi-Esan wanda ita ce shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Dr. Yemi-Esan ta bi taron ne daga ofishinta a Abuja, ba tare da ta je fadar Aso Rock ba.

Kara karanta wannan

Babu Shugaba Da Kuke Suka Irin Buhari A Tarihin Najeriya, Fadar Shugaban Kasa ta Caccaki Yan Jarida

Ministoci da-dama sun halarta

Alhaji Lai Mohammed; Abubakar Malami SAN; Mohammed Bello, Dr. Isa Ali Ibrahim Patanmi, Sadiya Umar Farouq suna cikin ministocin da aka gani a taron.

Haka zalika akwai Babatunde Raji Fashola SAN; Sunday Dare; Mahmood Abubakar; Sanata Hadi Sirika; Mohammed Abdullahi sai kuma Mu’azu Sambo Jaji.

Clement Agba, Ramatu Aliyu, Ademola Adegoroye, Goodluck Nana-Opia sun je wajen taron da kafansu.

Osinbajo ya je asibiti a Legas

A lokacin, an ji cewa Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya fitar da jawabi, yace Yemi Osinbajo yana fama da wani ciwon kafa tun tuni.

Hakan ta sa Farfsa Osinbajo ya je asibiti domin ayi masa aiki ya huta. Kusan ba a taba jin labari cewa Osinbajo mai shekara 65 a Duniya, bai da lafiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel