Za Ayi Shari’a a Gaban Alkali da Shugaba Buhari da Ministoci da Jami’an Gwamnati

Za Ayi Shari’a a Gaban Alkali da Shugaba Buhari da Ministoci da Jami’an Gwamnati

  • Wani Lauya ya yi karar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kotu saboda yadda ake gudanar da hukumar NDDC
  • Tun a wancan makon ne Barista Felix Ekengba ya kai kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1458/2022 a kotun tarayya na Abuja
  • Sauran wadanda za ayi shari’ar da su sun hada AGF watau Abubakar Malami SAN da Ministan Neja-Delta, Umana Umana

AbujaJaridar This Day ta rahoto za ayi shari’a da shugaba Muhammadu Buhari da wasu mutum uku a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja.

An kai karar shugaban Najeriyan da wasu Ministocinsa da kuma jami’an gwamnatin tarayya a kotu bisa zargin yi wa hukumar NDDC ta kasa katsalandan.

Wani Lauya mai suna Felix Ekengba ya shigar da wannan kara, yana fadawa kotu cewa wadanda ake tuhuma suna yi wa NDDC shiga sharo-babu shanu.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

Tribune tace Lauyan wanda da mazaunin Abuja ne, ya shigar da karar ne a karshen makon da ya wuce, yana tuhumar Ministan harkar Neja-Delta da laifi.

Korafin Felix Ekengba a kotu

A wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1458/2022, Lauyan yana so Alkali ya hana shugaban kasa, da sauran wadanda ake kara taba hukumar NDDC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna Ekengba ya kafa hujja da sashe na 4 na kundin tsarin mulki da sashe na 2 na dokar da ta kafa NDDC a 2000 wajen cin ma manufarsa.

Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya a jirgi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewarsa, dokar Najeriya ba ta bada dama wani ya shiga hurumin majalisar da ke kula da NDDC ba, muddin ba ayi wa dokar kwaskwarima a majalisa ba.

Idan Lauyan ya yi nasara a kotu, Alkali zai hana shugaban kasa, Ministoci da ma’aikatun gwamnatin tarayya iko da hukumar ko wani ma’aikacinta.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Daga cikin korafin Lauyan shi ne shugaban kasa ya canza dokar NDDC ta yadda aka ba sakataron din-din-din iko wajen katsalandan a aikin da ba na su ba.

Yadda shari'ar za ta kasance

Abubakar Malami SAN, Ministan Neja-Delta watau Umana Umana da ma’aikatar Neja-Delta da sakataren din-din na ma’aikatar za su kare kan su a kotu.

Rahoton The Nation yace har yau ba a tsaida lokacin da Alkali zai fara sauraron karar ba.

Sakamakon jarrabawar WASSCE

An ji labari Hukumar tattara alkaluma watau NBS ta fitar da bayanai a game da sakamakon jarrabawar WASSCE tun daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Sakamakon jarrabawar WASSCE na shekarun da suka wuce ya nuna jihohin Arewa da na Kudu maso yamma ne suka fi rashin yin abin kwarai a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel