An Yiwa Mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem Dashen Koda Cikin Nasara

An Yiwa Mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem Dashen Koda Cikin Nasara

  • Daga karshe likitoci sun yiwa fitaccen mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem aikin dashen koda
  • An yiwa Eedris aiki cike da nasara bayan matarsa, Yetunde Sekinat ta bashi gudunmawar kodarta guda daya
  • Jama'a sun taya ma'auratan murna kan nasarar da aka samu wajen aikin yayin da suka yi masu fatan alkhairi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Likitoci sun yiwa shahararren mawakin nan na Najeriya, Eedris Abdulkareem, dashen koda cikin nasara.

A watan Yuli ne mawakin ya bayyana cewa yana fama da cutar koda, inda hakan ya sa masoyansa da shahararrun yan uwansa suka tallafa masa da kudade.

Legit.ng Hausa ta kuma rahoto a baya cewa matar mawakin, Yetunde Sekinat ce ta basa gudunmawar kodarta.

Eedris da matarsa
An Yiwa Mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem Dashen Koda Cikin Nasara Hoto: @abdulkareemeedris
Asali: Instagram

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 22 ga watan Agusta, wani na hanun daman mawakin, Myke Pam, ya bayyana cewa an yi masa dashen kodan cikin nasara.

Kara karanta wannan

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Pam ya kuma mika godiya ga duk mutanen da suka tallafawa mawakin a lokacin da yake fama da gwagwarmayar rashin lafiyarsa.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Cike da tarin farin ciki da dumbin godiya ne mahukunta na kamfanin Lakreem Entertainment ke sanar da labarin nasarar da aka samu wajen yiwa mawakin Hip Hop na Najeriya kuma dan gwagwarmaya Eedris Abdulkareem aikin dashen koda a hukumance da wacce ta bashi gudunmawar koda-jajirtacciyar matarsa YT, yan awanni da suka wuce.”

Ya kuma mika godiya ga daukacin al’ummar Najeriya na gida da waje da masoyansa wadanda suka taimaka da addu’o’insu ga wadannan ma’aurata wadanda a lokacin da suke halin jinya.

Jama'a sun yi martani

Emma Iheme ya ce:

"An gode Allah!!!"

Cecil Iko ya yi martani:

"Godiya ta tabbata ga Allah. ina taya ka murna yallabai."

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Babafryo Igweh ya ce:

"Ma shaa Allah godiya ta tabbata ga Allah. Ina yi maka da matarka fatan samun sauki. Allah ya albarkaci eedris da iyalinsa."

Oluwakemi Harding ya ce:

"Wowwww an gode Allah ina yi masu fatan samun lafiya."

Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

A baya mun kawo cewa a ranar Asabar, 13 ga watan Agusta ne, abokai da takwarorin shahararren mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem, suka taru don karraman shi, ayyukansa da kuma taimakawa wajen sanar da duniya halin rashin lafiya da yake ciki a yanzu.

Eedris, ya samu yabo sosai daga mutane da dama da suka yi magana kansa a wajen taron da aka shirya don tunawa da shekarun da ya sadaukar wajen yin gwagwarmaya.

Mawakin wanda ke fama da rashin lafiya da ya shafi koda shima da kansa ya yi magana a wajen taron da aka shirya a saboda shi, yayin da ya yi godiya ga dukkan mutanen da suka taru don taya shi murna da kuma goya masa baya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Matar Gwamna Mummunan Farmaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel