Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

  • Daya daga cikin kwamandojin yan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna na kokarin auren daya
  • Dan'uwan wannan yarinya ya bayyana cewa da kyar yake iya cin abinci ko yin barci
  • Ranar 28 ga Maris, 2022 ne yan bindiga suka dasa Bam titin jirgin Abuja zuwa Kaduna suka kashe mutum 8 kuma suka kwashe gommai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - A ranar Juma'a, Tukur Mamu, jagoran sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan wadanda suka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya bada sanarwa mai tada hankali.

Mamu ya bayyana a wani bidiyo cewa shugaban ‘yan bindigan na shirin auren wata daga cikin fasinjojin jirgin mai suna Azurfa Lois John.

Azurfa Lois John dai yar shekara 21 ce mai karatu a tsangayar ilimin aikin noma a jami'ar jihar Kaduna KASU.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindigan da Suka Dauke Fasinjojin Jirgin Kasa na Shirin Aure ‘Yar shekara 21

Yayin da yake bada sanarwar sakin wasu mutane hudu a jiya, ‘dan jaridar ya fadakar da mutane cewa ‘yar autar da ke tsare ta na fuskantar barazana.

Azurfa Brother
Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

HumAngle ta yi hira da 'dan uwanta, Moses Ballie, wanda ya bayyana irin halin kuncin da suke ciki sakamakon halin da 'yar uwarsa ke ciki hannun yan bindigan.

A cewarsa:

"Ta tafi hutu Abuja ne sakamakon yajin aikin ASUU. Sai nace ta dawo Kaduna ta fara kasuwanci saboda da yajin aikin ya ki karewa."
"Da kyar nike iya barci kuma bana iya cin abinci. Cikin dare sai in tashi ina tunanin halin da suke ciki."
"Mun shiga mugun hali. Muna addu'a dai kuma mun yi imani da Ubangiji."

Moses ya bayyana cewa shine yanzu matsayin Uba ga Azurfa saboda iyayensu sun mutu a 2020.

Kara karanta wannan

Buhari ga jami'ai: Ku tabbata kun kawar 'yan ta'addan Najeriya gaba daya

Jiya an sako mutum hudu

A jiya aka samu labarin an kubutar da Mama Halimatu Atta mai shekara 90 da kuma ‘diyarta, Hajiya Adama Atta Aliyu bayan sun yi kwanaki 144 a cikin jeji.

Sauran wadanda aka fito da su jiya su ne: Mohammed Sani Abdulmaji (M.S Ustaz) da Modin Modi Bodinga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel