Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

  • Ba sabon labari bane cewa fitaccen mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem, ya kamu da ciwon koda kuma yana ta kwanciya a asibiti
  • Eedris da kansa ya je shafukansa na soshiyal midiya don bayyana cewa tuni aka fara yi masa wankin koda yayin da ake neman wanda zai bashi nasa
  • A yayin wani taro da aka yi a kwanan nan saboda mawakin, an bayyana cewa matar mawakin Shekinat Yetunde ce za ta bashi kodarta
  • Haka kuma, a wajen taron an bayyana abun da aka tara don tallafawa mawakin yayin da yake fama da rayuwarsa

Najeriya - A ranar Asabar, 13 ga watan Agusta ne, abokai da takwarorin shahararren mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem, suka taru don karraman shi, ayyukansa da kuma taimakawa wajen sanar da duniya halin rashin lafiya da yake ciki a yanzu.

Eedris, ya samu yabo sosai daga mutane da dama da suka yi magana kansa a wajen taron da aka shirya don tunawa da shekarun da ya sadaukar wajen yin gwagwarmaya.

Eedris Abdulkareem da matarsa
Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta Hoto: @abdulkareemeedris
Asali: Instagram

Mawakin wanda ke fama da rashin lafiya da ya shafi koda shima da kansa ya yi magana a wajen taron da aka shirya a saboda shi, yayin da ya yi godiya ga dukkan mutanen da suka taru don taya shi murna da kuma goya masa baya.

Ya yi godiya ga Dede Mabiaku, Baba Keke, Jude Orhorha, Myke Pam da Lakreem All-stars, ya kuma saki sakon jinjina ta musamman ga mutum na musamman a rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mawakin wanda bai samu zuwa wajen taron da kafarsa ba amma ya yi magana ta yanar gizo, ya yi dadadan zantuka kan matarsa Yetunde Sekinat Abdulkareem yana mai godiya a gare ta kan bashi kodarta da ta yi ba tare da ta barsa ba.

Eedris a yayin jawabinsa na godiya ya ce:

“Ina godiya ga kowa da kowa, nagode da soyayyarku da goyon bayanku, nagode maku dukka, nagode nagode kuma Allah ya albarkace ku. Baba Dede Mabiaku, Abdulganiu, Sis Shola, Sis Mariam, ku san duk Lakreem all-star, Jahman Anikulapo-Kuti, Baba Keke Ogungbe, dukkanin mutanen da ke nan nagode maku.”

Bayan ya godema mutanen da suka halarci taron sai ya kuma ci gaba da baiwa masoyansa da magoya baya tabbacin cewa yana da yakinin samun lafiya. Ya kuma jadadda cewa da izinin Allah madaukakin sarki zai fito cike da karfi bayan an yi masa aiki.

Daga nan sai ya aike sako na musamman ga matarsa yana mai cewa:

“Ina mai kuma jinjinawa matata Sekinat Yetunde Abdulkareem, Allah ya yi maki albarka sahiba. Ina nufin, na san yadda tsarin yake, da zai kai ni tsawon akalla shekara daya ko biyu, wa ya san wani lokaci zai dauka kafin na samu mai bani koda saboda likitocin sun ce basa karfafa cire kodan siyarwa.”

Eedris ya bayar da dan takaitaccen labara a yayin jawabin nasa game da yadda matarsa ta yanke shawarar bashi kodarta, karanta labarin a kasa:
“A karon farko da muka je ganin likita, likitan ya bayyana cewa basa karfafa cire koda da siyar da sassan jikin mutum, cewa dole wanda zai bayar da kodarsa ya zama dan uwa, aboki, ko diya ko dan uwanka ko danka. Bayan likitan ya fadi haka, nan take matata ta yanke shawarar yin dukkanin gwajin.
"Duk gwaje-gwajen da tayi komai ya fito da kyau cewa ta yi daidai da ni. Saboda da wannan ina mika godiya ga Allah kuma nagode Allah ba sai nay i dogon jira ban a shekara daya ko biyu saboda na san ba abu mai sauki bane samun wanda zai bayar da nashi. Wannan ne dalilin da yasa nake son godewa matata.”

Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce

A wani labarin, wata matashiyar mata mai suna Misis Zanga a Twitter ta wallafa wasu hotuna don yabawa mijinta.

Matar a cikin wallafar da ta yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta, ta bayyana cewa mijinta yana taimakonta sosai da sosai.

Ta yi godiya ga Allah da ya bata mutumin a matsayin abokin rayuwa. A cikin hotunan, an gano mutumin ba riga yana taimakawa matar a cikin dakin girki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel