Ko Shakka Babu Zan Auri Mace Fiye Da Daya, Basarake Mai Shekaru 19

Ko Shakka Babu Zan Auri Mace Fiye Da Daya, Basarake Mai Shekaru 19

  • Matashin sarki da yafi kowani basarake karancin shekaru a Najeriya, Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare ll, ya ce zai auri mace fiye da guda daya
  • Basaraken ya ce auren mace fiye da guda daya wajibi ne gare shi kamar yadda yake bisa al’adarsu
  • Oba Adeyeoba ya ce duk da haka baya da muradin yin aure a yanzu sai zuwa gaba idan ya kara girma domin a yanzu yana kunyan magana da mata

Ondo - Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare ll Arujale Ojima na Okeluse, da ke karamar hukumar Ose ta jihar Ondo ya ce zai aure mace fiye da kuda daya kamar yadda al’ada ta tanadar.

Sarkin mai shekaru 19 wanda ya kammala makarantar sakandare kwanan nan, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsoho mai shekaru 66 ya kama tallan mangoro don tara kudin maganin matarsa

Matashin Basarake
Ko Shakka Babu Zan Auri Mace Fiye Da Daya, Basarake Mai Shekaru 19 Hoto: religionigeria.com
Asali: UGC

Basaraken ya bayyana cewa auren mace fiye da guda daya wajibi ne ga duk mutumin da ya zama sarki saboda matarsa ta fari idan ta haifi namiji shine zai zama sarki nag aba sannan dan mata ta biyu ya zama abun da ake kira Eleki.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Eh wajibi ne na auri mace fiye da daya. A al’adarmu na nan, wajibi ne sarki ya mallaki matar aure fiye da daya saboda matarsa ta farko, idan tana da yaro namiji, shine zai zama sarki na gaba sannan dan farin matar ta biyu shi zai zama abun da muke kira Eleki sannan idan uwargidarsa bata da yaro namiji sannan matarsa ta biyu na da shi, to dan farin matar ta biyu ne zai zama sarki nag aba.
"Eleki shine mutum na biyu mai fada aji bayan sarki; idan sarki baya nan, shine yake jar ragamar mulki.”

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Akinghare, wanda shine Basarake mafi karancin shekaru a Najeriya, ya kuma bayyana cewa yana da abokai mata amma yana jin kunyan yiwa mata magana.

Shafin LIB ya kuma nakalto yana cewa:

“Ina da su da yawa, amma ina so na kara girma sannan na kara balaga kafin na fara hulda da mata, ina nufin aure. A yanzu bana son magana da mata, don haka neman soyayyar mace yana da wahala a gareni saboda idan ka ganni za ka san ni mutum ne mai kunya.”

Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

A wani labarin, wani tsoho dan shekaru 90 mai suna Baizirre Jean Marie ya bayyana cewa har yanzu a kasuwa yake baida aure.

Kafar labarai ta Afrimax English ta ziyarci kauyen mutumin kuma sun zanta da shi, inda ya bayyana matsayinsa a soyayya.

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

Baizire ya bayyanawa kafar labaran cewa ya tsaya ne a aji biyar na makarantar firamare, wanda yace bai tsinana masa komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel