'Ana Shirin Kashe Ni' Yakubu Dogara Ya Aike Da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye

'Ana Shirin Kashe Ni' Yakubu Dogara Ya Aike Da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye

  • Yakubu Dogara ya aike da korafi ga Sufeta Yan sanda na ƙasa kan wasu da ake zargin suna kulla shirin raba shi da rayuwarsa
  • Tsohon kakakin majalisar tarayyan ya bayyana sunayen yan sanda uku da suka yi kokarin siyarwa wani bindiga da nufin kashe shi
  • Tuni dai yan sanda suka kama jami'an uku kuma yanzu haka ana tuhumarsu a sashin binciken manyan laifuka

Bauchi - Tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Yakubu Dogara, ya aike da sakon shigar da korafi ga Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan, Alƙali Usman, kan yunkurin da ake na kashe shi.

Ya kuma yi zargin cewa baya ga shi, masu mummunan nufin na harin rayuwar wasu mutum uku, cikin su har da shugaban CAN na ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa.

Dogara, wanda ke wakiltar mazaɓar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro, ya faɗi haka ne a wata takardar shigar da ƙorafi da ya tura kai tsaye ga IGP na ƙasa, wakilin Punch ya ci karo da ita ranar Asabar a Bauchi.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Yakubu Dogara.
'Ana Shirin Kashe Ni' Yakubu Dogara Ya Aike Da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya tura kwafin takardar ga Mai ba da shawara kan tsaro, Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya DSS, kwamishinan yan sandan jihar Bauchi da Daraktan DSS na Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar na ɗauke da ranar 18 ga Agusta, 2022 da kuma taken, "Kira domin gudanar da bincike kan yawon bindiga tsakanin Insufecta, Dakat Samuel, Inspector Auwalu Mohammed da Barau Joel Amos (Sarkin Yaki)."

"Lamarin na da alaƙa da amsa laifin Barau Joel Amos, inda ya nuna cewa ya nemi sayen bindiga da nufin hallaka ni da wasu mutum uku."

Wane mataki aka ɗauka kan yan sandan?

Dogara ya kara da cewa yan sanda uku da ya ambaci sunayen su a sama, yanzu haka suna ana binciken su kan zargin kokarin siyar da bindiga ga ɗaya daga mutanen mazaɓarsa.

Ɗan majalisar ya ce bindigar da ake magana akanta, a bayanan ɗan mazaɓarsa da ya amsa laifinsa, ya nemi mallakarta ne da nufin hallaka shi da wasu mutane uku.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

Daily Trust ta tattaro Wani sashin korafin ya ce:

"Ina mai jawo hankalinka kan wannan batun da na taɓo wanda yanzu haka yake kan teburin DCP na sashin binciken manyan laifuka a hukumar yan sandan Bauchi."
"Ina ganin labari ya zo gare ka saboda batun ya shafi satar makamai kuma waɗan da ke da alhakin tsare makaman ne ke da hannu da kuma mutum ɗaya daga ƴan mazaɓata, Barau Joel Amos, wanda ya nemi siyan bindiga daga jami'ai."
"Na shiga damuwa bisa rashin wata shawara daga hukumar yan sanda game da barazanar da ake wa rayuwarmu, wacce zata bamu damar ƙara tsaurara tsaro a tare da mu ko kula da motsin mu."

Daga ƙarshe, tsohon kakakin majalisar wakilan ya roki shugaban hukumar yan sanda na ƙasa da a ɗauki lamarin dagaske, bai kamata a barshi haka nan sakaka ba.

A wani labarin kuma Wani Ɗan Jam'iyyar APC Ya Bindige Mutum Hudu a Babban Shagon 'Supermarket'

Kara karanta wannan

Tinubu da APC Za Su San Matsayar Takararsu, Kotu Ta Sa Ranar Fara Shari’a

Wani mutumi da ake tsammanin ɗan daban siyasa ne ya bindige mutum huɗu a babban shagon Super Market a jihar Ondo.

Ɗan daban wanda ake wa laƙabi da, Para, ɗan APC, ya yi kaurin suna wajen yi wa mutane kwace ta dole a yankin karamar hukumar Idanre.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel