Wasu ’Yan Bindiga Sun Bi Har Gida, Sun Hallaka Wani Lauya a Zamfara

Wasu ’Yan Bindiga Sun Bi Har Gida, Sun Hallaka Wani Lauya a Zamfara

  • Wani rahoton da ke fitowa daga jihar Zmafara ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun hallaka wani lauya mai suna B.T. Azza Esq
  • Abokan aikinsa sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma yi kira ga jami'an tsaro su yi bincike don gano makashin abokinsu
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta sake jaddada manufarta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma

Gusau, jihar Zamfara - Wasu miygun 'yan bindiga sun bindige lauya a birnin Gusau na jihar Zamfara a ranar Alhamis din da ta gabata.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun shiga gidan Barista Benedict Azza da ke unguwar Saminaka, a Gusau, inda suka yi yunkurin sace shi.

Majiya ta bayyana cewa, an lauyan ya yi gwagwarmayar shiga motarsa da nufin ya tsere, amma 'yan bindiga suka harbe shi har sau uku.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yaudari manoma duk da kulla yarjejeniyar zaman lafiya, sun sace 16

Yadda wasu 'yan bindiga suka harbe wani lauya a jihar Zamfara
Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka wani lauya a Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Barrista Junaidu Abubakar, na kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 19 ga watan Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abokinsa ya ba da labarin yadda aka kashe shi

Junaidu ya ce, an tsinci ganwar Barista ne a kusa ofishin jami'an hukumar kiyaye haddura ta kasa da ke kan titin bye-pass bayan tsagerun suka hallaka shi, rahoton jaridar Guardian.

A cewarsa:

“Jiya da misalin karfe 12:30 na dare, ina gidana naga kiran wasu abokan aikinmu uku suna sanar da ni cewa wasu 'yan bindiga sun harbe B.T. Azza Esq, kuma ga can gawarsa a kwance a bakin titi a hanyar bye-pass kusa da ofishin FRSC da ke Gusau."

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Mohammed Shehu, ya shaidawa majiyar cewa yanzu dai ana ta bincike don gano tushen mutuwar Barista.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Yana Neman Kashe Tsohon Shugaban Majalisa

Hakazalika, jami'in ya kara wa mazauna karfin gwiwar cewa, 'yan sanda a fadin jihar sun dukufa domin tabbatar da kare rayukan mazauna.

Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

A wani labarin, daya daga cikin wadanda aka ceto daga harin jirgin kasar Abuja-Kaduna, Hassan Usman, ya ce har yanzu shi dan gani kashe nin Shugaba Muhammadu Buhari ne, The Punch ta rahoto.

Kafin sakinsa a ranar 25 ga watan Yuli, Usman, wanda lauya ne, da matarsa Amina suna cikin fasinjojin da aka sace yayin harin ranar 28 ga watan Maris.

Usman ya shafe fiye da kwanaki 100 a hannun yan ta'adda kuma yana cikin wadanda aka gani a bidiyo yan ta'adda na yi musu bulala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel