Wani Dan Daban Siyasa Ya Bindige Mutum Hudu a Cikin Kasuwa a Jihar Ondo

Wani Dan Daban Siyasa Ya Bindige Mutum Hudu a Cikin Kasuwa a Jihar Ondo

  • Wani mutumi da ake tsammanin ɗan daban siyasa ne ya bindige mutum huɗu a babban shagon Super Market a jihar Ondo
  • Ɗan daban wanda ake wa laƙabi da, Para, ɗan APC, ya yi kaurin suna wajen yi wa mutane kwace ta dole a yankin karamar hukumar Idanre
  • Hukumar yan sanda ta ce rahoton da ta samu ga nuna lamarin na fashi da makami ne kuma ta kama wanda ake zargi

Ondo - Wani da ake kyautata zaton ɗan daban siyasa ne ya harbi aƙalla mutum huɗu da bindiga a garin Idanre, hedkwatar karamar hukumar Idanre, jihar Ondo.

Jaridar Leadership ta gano cewa ɗan daban, mamban jam'iyyar APC, ya kutsa kai babban shagon kasuwanci, 'Supermarket' a yankin Ojota da nufin yi wa mai wurin fashi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Taswirar jihar Ondo.
Wani Dan Daban Siyasa Ya Bindige Mutum Hudu a Cikin Kasuwa a Jihar Ondo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mutumin da ake zargin, wanda ya fi shahara da sunan, 'Para' ya yi ƙaurin suna wajen yi wa mutanen yankin kwace bisa tilas yayin da gwamnati ta kawar da kanta daga abinda yake aikata wa.

Wata majiya ta faɗa wa jaridar cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A ko da yaushe Para ya saba aikata irin haka kuma gwamnati bata taɓa sa masa ido ba. Yau ya shiga babba shagon Super Market don ya karɓi kudi amma masu wurin suka hana shi."
"Mai shagon ya gaya masa cewa yanzun suka fito da safe ba su fara ciniki ba. Lokacin da suka fara sa'insa da mai wurin, nan take Para ya fizgi jakar mai shagon, suka fara ja-in-ja da shi kan jakar."
"Kafin mu gano me ke faruwa, Para ya zare bindiga ya harbi mutum huɗu nan take. Tuni aka yi saurin kai mutanen Asibitin Idanre, inda yanzu haka suna kwance ana ba su kulawa."

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa da Matafiya da Dama a Jihar Arewa

Shin hukumomin tsaro sun samu rahoto?

Amma da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Funmi Odunlami, ya ce Kes din na fashi da makami ne, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Odunlami ya bayyana cewa tuni jami'an yan sanda suka garzaya suka cafke wanda ake zargi da aikata lamarin.

Kakakin yan sandan ya ce, "Mun samu rahoton fashi da makami kuma wanda ake zargi na tsare a hannun mu yanzu haka."

A wani labarin kuma Sojoji Sun Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa

Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Oladayo Amao, ya ce haɗin kan hukumomin tsaro ya haifar da gagarumar nasara.

A cewarsa, samamen da sojoji suka kai mafakar yan ta'adda ta sama da ƙasa a shiyyoyin arewa uku ya halaka manyan yan tada ƙayar baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel