Jami'ar Gombe ta yi watsi da yajin ASUU, ta nemi dalibai su dawo karatu

Jami'ar Gombe ta yi watsi da yajin ASUU, ta nemi dalibai su dawo karatu

  • Hukumar gudanarwar jami'ar jihar Gombe ta yi watsi da yajin aikin ASUU, ta kira dalibai su dawo karatu, tare da kamma zangon farko
  • Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta shafe watanni shida tana yaji saboda biris da gwamnati ta yi na biyan wasu bukatun mambobinta
  • Jami'o'in jiha a kasar nan da daga cikin wadanda yajin aikin ya shafa, duk dai ana neman yadda lamurra za su yiwa malamai ne dadi

Tudun Wada, jihar Gombe - Jami'ar jihar Gombe (GSU) ta yi kira ga daliban aji daya da su gaggauta dawowa makaranta domin kammala rajista, kana su kare karatun zangon farko na 2021/2022 da aka fara.

Jami'ar ta fara rajistar daliban aji daya kafin fara yajin aikin ASUU a watan Fabrairu, lamarin da ya kawo tsaiko ga rajistar da ci gaba da karatun zangon.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

A wata sanarwa da aka aikowa wakilin Legit.ng Hausa, jami'ar ta ce ta yi shawari, ta kuma amince daliban su dawo domin ci gaba da karatu.

Jami'ar Gombe ta koma karatu duk da yajin ASUU
Jami'ar Gombe ta yi watsi da yajin ASUU, ta nemi dalibai su dawo karatu | Hoto: hotels.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar da ke dauke da sa hannun Mataimakin magatakardan jami'ar, Musa Sarki:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sakamakon tuntubar juna da aka yi tsakanin masu ruwa da tsaki a jami’ar, an kuduri aniyar baiwa daliban aji 1 damar dawowa makaranta a ranar Litinin 22 ga watan Agusta, 2022 don kammala rajistarsu, a rantsar dasu kana su kammala zangon karatu na farko, 2021/2022.
"Saboda haka, duk daliban aji 1 za su hallara ga tsangayoyin katayunsu a ranar Litinin, 22 ga Agusta, 2022."
Jami'ar Gombe za ta koma karatu duk da yajin ASUU
Jami'ar Gombe ta yi watsi da yajin ASUU, ta nemi dalibai su dawo karatu | Hoto: Bashir Sa'idu
Asali: UGC

ASUU ce ta umarci yajin aiki, don haka ita ce za ta kira mu koma aiki

Da take tabbatar da wasikar daga mahukuntan jami'ar take, malamar jami'ar ta GSU da ta nemi a sakaya sunanta saboda kare aikinta, ta yi karin haske game da yiwuwar komawar ma'aikata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Hare-hare sun munana, an garkame dukkan makarantu a Jigawa

Ta ce, kungiyarsu ta malaman jami'a ce ke da ikon kira a koma karatu, don haka ko da hukumomin jami'a sun nemi a dawo, dole su jira meye kungiyar ta ASUU za ta ce

Ta ce:

"Yajin aiki dai ASUU ce ta umurci ayi, saboda haka su yakamata su kira, ba hukumomin gwamnatin jiha ba ko hukumar jami'a. Muna jira muji meye ASUU zasu umurce mu dayi.
"Suna meman su kwaba alamura ne kawai. Amma sunsan ba haka ake kiran yanje yajin aiki ba."

Hakazalika, ta yi tsokaci da cewa, kiran da jami'ar Gombe ke yi na komawa wani yunkuri ne na hada mambobin ASUU reshen jihar da kuma uwa kungiyar ta kasa.

A cewarta:

"Na yi imanin suna son mu koma ne saboda batun da karin albashi da ASUU ta kasa keyi. To, don haka zasu wulakanta mu yadda sukeso, ganin cewa ASUU ta kasa baki daya ba za su goyi bayanmu ba muddin akace mun koma aiki."

Kara karanta wannan

Babu haske: An kammala ganawar gwamnatin Buhari da ASUU, sakamako bai yi dadi ba

Ta kuma shaida cewa, babu bambanci tsakanin ASUU reshen jiha ko kasa, duk abu daya ne.

Ta kuma ba da misali da cewa:

"Misali, batun tsarin alawus-alawus da malami ke samu da akayi amince dashi shekarun da suka gabata ai yana da alaka da jami'o'in jiha, duk jami'ar jihar dake da matsa da gwamnatin jiha sai ASUU a matakin kasa tayi taka tsantsan na tabbatar da cewa samu mafita."

Gwamnati bata damu ba, ganin yadda ake bude sabbin jami'o'i

Da wakilinmu ya tambayi ko akwai wata hanya da za a iya bi ban da yajin aiki wajen biyan bukatun ASUU, malamar ta ce:

"Ganin yadda ake tafiya a mulkin Najeriya, duk abu cikin lumana ba a samun matsaya. Kamar yajin aikin ne kawai yake sakawa su duba lamari.
"Kuma yana da kyau jama'a su fahimci cewa kafin akai ga yin yajin aiki sai an bi matakai da yawa."

Da take cewa gwamnati bata damu da karatun jami'a ba, ta ce:

Kara karanta wannan

Assha: Darajar Naira ta sake raguwa a kasuwar hada-hadar canjin kudade

"Duba da yawan yadda gwamnati ke amincewa da bude sabbin jami'o'i masu zaman kansu, ya nuna cewa basu damu ba. Gwamnati tana son a maida karatun jami'a ya koma kamar yadda makarantun sakandare da firamare suka dawo a lalace."

Sai dai, wani malamin jami'ar Bashir Sa'idu ya ce bai da zabi, duk abin da hali ya yi shi za a dauka.

"Gaskiya ba abinda zan iya fada akai. Sai abinda hali yayi. Ba abinda za a yanke hukunci lakaci guda bane."

Ganawar ASUU da FG Ta Kammala, Ba a Cimma Wata Matsaya Ta Kirki Ba

A wani labarin, a ranar Talatar da ta gabata ne aka gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin Buhari, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa tawagar gwamnatin tarayya ta gana da wakilan kungiyar ASUU a hedikwatar hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta NUC.

Kara karanta wannan

Yajin ma'aikatan wuta: Gwamnati da TCN na rokon kada a sa 'yan Najeriya a duhu

A cewar majiyar daga ASUU: “Ganawar da tawagar FG ta kasance karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs kuma an fara da karfe 12:00 na rana, an kammala da karfe 3:00 na rana. Babu wani sabon tayi a teburin, kawai dai sun roke mu mu janye yajin aikin ne.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel